'Yanbindiga sun kashe 'yanjarida da ɗansanda a Haiti
Akalla 'yanjarida biyu aka kashe da dansanda daya a Haiti lokacin da gungun wasu 'yanbindiga ya bude wuta a wajen taron manema labarai na sake bude asibitin gwamnati mafi girma a babban birnin kasar, Port- au- Prince.
Hadakar gungun kungiyoyin 'yanbindiga da ke da iko da yawancin birnin ne ta kai harin.
'Yanjaridar na jiran zuwan ministan lafiya na kasar ne Dr. Duckenson Lorthé Blema a wajen taron sake bude babban asibitin lokacin da kwatsam 'yanbindigar suka bude wuta.
Mutane da dama sun ji rauni kafin a tura karin ma'aikatan tsaro wajen domin kai dauki.
Kungiyar 'yandaba da ake kira Viv Ansanm ta sanya wani hoton bidiyo a intanet tana ikirarin kai harin.
A cikin bidiyon kungiyar wadda a da asibitin ya fada hannunta ta kuma yi kaca-kaca da shi a watan Maris, kafin gwamnatin kasar ta Haiti ta sake kwato shi, ta ce ba ta bayar da izinin sake bude asibitin ba.
A watan Yuli ne gwamnatin ta kwato asibitin daga hannun kungiyar ta 'yandaba da ke da iko da yawancin sassan babban birnin.
A wata sanarwa da ya yi ta wani bidiyo shugaban gwamnatin rikon-kwaryar kasar, Leslie Voltaire, ya yi suka ga harin.
Ya ce, ''abin da ya faru a yau ranar Kirsimeti, a babban asibitin inda jama'a, inda 'yanjaridar, inda jami'an 'yansanda suka kasance wadanda aka kai wa harin, abu ne da ba za a lamunta da shi ba.
Muna tausaya wa iyalan dukkanin wadanda aharin ya rutsa da su, musamman ma rundunar 'yansandan Haiti da dukkanin kungiyoyin 'yanjarida. Muna ba su tabbacin cewa wannan hari ba zai tafi a banza ba.'' In ji shi.
Al'ummar kasar ta Haiti na ci gaba da dandana kudarsu da tashin hankali – da ya hada da kisan gilla da fyade da satar jama'a da kwace na kungiyoyin 'yandaba, duk da kafa sabuwar gwamnati ta rikon kwarya da aka yi a watan Afirilu da kuma samar da rundunar 'yansanda ta kasashe karkashin jagorancin 'yansandan Kenya wata shida baya, domin tabbatar da tsaro.
Haiti ta fada cikin tashe-tashen hankali na inna-naha tun bayan kisan gillar da aka yi wa tsohon shugaban kasar, Jovenel Moïse, a 2021.
An yi kiyasin cewa har yanzu kusan kashi 85 cikin dari na babban birnin kasar, Port-au-Prince har yanzu yana hannun kungiyoyin 'yandaba.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce an kashe akalla mutum dubu biyar a tashe-tashen hankali a kasar, a wannan shekarar ta 2024 kadai, kuma ta ce kasar a yanzu na dab da durkushewa.