Tsare Sirri
Gabatarwa da kuma kaidoji
BBC a shirye take ta kare ka tare da bayananka a lokacin da kake amfani da shafinta. Domin mu samar maka da dinbin aikace aikacen BBC, a wasu lokutan za mu nemi sanin wasu bayananka.
Duk lokacin da ka bada wadannan bayanai, muna da ikon yin amfani da su kamar yadda tsarin shari'a na Birtaniya ya tanada, wanda ya hada da kundin kare bayanai na 1998.
Shafin yana dauke da rariyar likau dake hada shi da sauran shafuka mallakar wasu. BBC ba ta da alhakin abinda ke kunshe a wadannan shafuka, don haka idan ka shiga to ka sani kai ka kai kanka ba ruwan BBC.
Wadanne bayanai BBC za ta tattara dangane da ni?
Idan ka amince ka shiga ko ka karbi bayanai daga shafin BBC, kamar labarai ta e-mail, mukala da gasa da tattauanawa ta kai tsaye ko kuma dandalin sakonni, to za mu nemi sanin bayanan ka. Bayanan za su hada da sunanka da adreshinka na E-mail da lambar wayar salula ko kuma ta gida ko kuma ranar haihuwa.
Idan ka rubuta bayanan ka a inda aka nemi ka yi hakan, ka bawa BBC da masu yi mata ayyuka damar baka bayanan da ka nema.
Har ila yau BBC na amfani da Cookies. Cookies wata karamar hanya ce ta tattara bayanai game da abinda ka fi so wanda zai bamu damar juya akalar shafin domin dacewa da ra'ayinka. Za ka iya sa mashigar Internet dinka ta amince da baki dayan cookies ko kuma su yi watsi da su a kowanne lokaci.
Hakazalika, muna tattara adireshin IP (Adireshin IP shi ne lambar da za ta bayyana wata kwamfiyuta a cikin intanet).
Muna amfani da dabarun masu sharhi domin duba adireshin IP da Cookies domin inganta yadda kake amfani da shafin. Wadanann bayanai ba za a yi amfani da su ba wajen hada bayananka na sirri.
Za a kuma dinga share wannan mashigar akai akai.
Haka kuma muna amfani da adreshinka na IP domin sanin ko kana amfani da shafin ne daga ciki ko wajen Burtaniya.
Idan shekarunka ba su haura goma sha shida ba, to ka nemi izinin mahaifanka kafin ka baiwa BBC bayananka na sirri. Wadanda ba su sami wannan izinin ba to ba su da damar bamu bayanansu na sirri.
Ta wacce hanya BBC suke amfani da bayanan da suka samu dangane da ni?
BBC za ta yi amfani da bayanaka ne kawai saboda wasu dalilai, wadanda suka hada "huldar aiki", abinda ke nufin cewa BBC za ta iya tuntubarka dangane da irin bayanan da ka nema.
Za mu boye bayanan ka cikin sirri, sai inda doka ta nemi a bayyana.
Idan ka rubuta ko ka aiko da bayanan da basu dace ba a ko'ina ko zuwa bbc.co.uk, ko kuma wata halayya da ba dace ba, BBC za ta yi amfani da bayananka na sirri wajen dakatar da wannan halayya.
Har tsawon yaushe ne BBC za ta rike bayanai na?
Za mu ajiye bayananka a na'urarmu har tsawon lokacin da ya dace domin yin abinda ya dace. A lokacin da ka bayar da gudummawa zuwa shafin BBC, za mu ajiye bayananka har na tsawon lokaci muddin dai akwai bukatar yin hakan.
Domin samun cikakken bayani kan manufar BBC game da kare bayanan sirrin jama'a, duba ainahin shafin turanci a: http://www.bbc.co.uk/privacy