Yadda ɗan'adam ke ƙoƙarin gano sirrin yadda aka halicci rana

Artist's impression of Parker Solar Probe spacecraft flying past the Sun

Asalin hoton, NASA

Bayanan hoto, Shirin bicken rana na Parker Solar Probe zai kafa tarihin zuwa wuri mafi kusa da rana
  • Marubuci, Rebecca Morelle
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Science Editor

Kumbon hukumar kula da sararin samaniya na Amurka (Nasa) na ƙoƙarin kafa tarihi na shirin kusantar ranar da ba'a taɓa yi ba.

Kumbon Parker Solar zai yi ƙoƙarin kusantar duniyar ranar tare da jure wa tsananin zafi da turiri.

Ya ƙatse sadarwa na wasu kwanaki a lokacin da yake tafiya mai tsananin zafi, a yayin da masu binciken kimiyya za su jira wani saƙo da zai turo wanda suke sa ran samu a ranar 27 ga watan Disamba domin sanin ko ya yi nasarar isa.

Fatan su shi ne wannan kumbon zai taimaka wajen ƙara fahimtar yadda ranar take aiki.

Dakta Nicola Fox, shugabar binciken kimiyya a Nasa ta shaida wa BBC cewa: ''an shafe ɗaruruwan shekaru ana nazarin duniyar rana, amma ba za a san yanayin wurin ba har sai an kai ziyara cikinsa''

''Don haka ba za mu iya sanin yanayin ranar har sai mun bi ta a inda take.''

Hoton rana daga sashen binciken rana na Nasa

Asalin hoton, NASA

Bayanan hoto, Kumbon zai isa sararin samaniyar rana na waje-waje

Kumbon Parker Solar wanda aka ƙaddamar a shekarar 2018, zai yi tafiya zuwa tsakiyar sararin samaniyar duniyoyin da ke maƙwaftaka da mu.

Tun a baya kumbon ya bi ta kusa da duniyar rana har so 21, kullum yana ƙara kusantar ta, amma wannan ziyarar ta ranar a jajibirin kirsmeti zai kafa babban tarihi.

A zuwan shi mafi kusa, kumbon ya kai mil miliyan 3.8 daga rana.

Hakan ba zai yi kama da ya yi kusa ba, amma Nicola Fox ta yi ƙarin bayani: ''muna da nisan mil miliyan 93 daga rana, misali, idan na kwatanta nisan duniyarm da duniyar rana a matsayin mita ɗaya, kumbon zai je wurin da ke da nisan sentimita 4 daga rana - hakan ya yi kusa''.

Kumbon zai buƙaci ya jure tsananin zafin rana da ya kai 1,400 a ma'aunin celcius, da zai iya lalata kayan laturoni da ke ciki.

Kumbon yana kuma da kariya a wajen shi mai ƙaurin inchi hudu da rabi, amma tsarin shi ne, ya shiga ya fita da saurin gaske.

A taƙaice, zai fi dukkan wani abu da ɗan-adam ya haɗa sauri, inda zai rinƙa tafiyar mil 430,000 cikin awa ɗaya - kwatankwacin tafiya daga Landan zuwa birnin New York a ƙasa da daƙiƙa 30.

Aurora borealis in Howick, Northumberland

Asalin hoton, PA Media

Bayanan hoto, ..

To, me ya sa za a yi duk wannan ƙokarin domin ''taɓa'' rana?

Masana kimiyya na fatan cewa a yayin da kumbon ya bi ta jikin rana, zai warware sarƙaƙiyar da aka daɗe ana ƙoƙarin ganewa.

''Wajen ranar na da matuƙar zafi, kuma mun kasa gano dalilin hakan,'' in ji Dakta Jennifer Millard, wata masaniya ilimin taurari da ke Wales a Birtaniya.

''Ɓangaren ranan da ake iya gani daga duniya na da zafin aƙalla maki 6,000 a ma'aunin salshiyas, yayin da wajen ranar da ake gani lokacin faɗuwar rana yana kai wa miliyoyin maki - kuma wannan ya fi nesa da rana. To ta yaya wannan wurin ke ta ƙara zafi?

Wannan zuwan nasu zai kuma taimaka wa masana kimiyya ƙara fahimtar yanayin zafin da ke fita daga rana.

Sai dai wannan yanayi zai iya janyo wasu matsaloli, kamar kawo tsaiko ga tashoshin wutar lantarki, kayan laturoni da kuma kayan sadarwa.

''Fahimtar duniyar rana, da ɗabi'unta, da yanayinta da kuma yanayin zafin da take fitarwa, yana da muhimmanci sosai ga rayuwarmu ta yau da kullun a nan doron duniya,'' a cewar dakta Millard.

Hoton tirirn da rana ke fitarwa daga sashen binciken rana na Nasa.

Asalin hoton, NASA

Bayanan hoto, Masana kimiyya na fatan wannan Kumbon zai taimaka wajen warware sarƙaƙiya da dama game da rana.

Masana kimiyya na hukumar Nasa na zaman jira cikin fargaba a lokacin kirsimeti, yayin da kumbon ya daina turo saƙonni zuwa duniyarmu.

Nicola Fox ta ce a da zarar ya turo saƙo zuwa duniya, tawagar za su aika mata sakon kar-ta-kwana domin sanar da ita cewa kumbon na lafiya.

Ta yarda cewa tana zaman ɗar-ɗar a kan wannan yunƙurin nasu na ƙarfin hali, amma kuma ta yarda cewa komai zai tafi daidai.

''Zan damu da kumbon. Amma kuma mun ƙera shi yadda zai jure wa dukkanin yanayi mai tsanani. Kumbo ne mai juriya sosai.''