Kaidojin amfani da shafi
BBC ce ke bayar da damar amfani da shafin bbc.co.uk' a cikin Burtaniya da kuma a sassa daban daban na duniya (masu amfani da shafin a wajen Burtaniya za su iya ganin tallace tallace a wasu shafuka wadanda sashen BBC mai gudanar da harkokin kasuwanci wato BBC Worldwide Limited (BBCW)) bisa wadannan ka'idoji:
Amfani da wannan shafin na nuni da cewa ka amince da ka'idojin wadanda ke fara aiki nan take da zarar ka shiga shafin bbc.co.uk. Idan ba ka amince da wadannan ka'idoji ba, to kada ka shiga ko yi amfani da shafin bbc.co.uk.
BBC za ta iya sauya wadannan ka'idoji daga lokaci zuwa lokaci a don haka sai ka rika duba wadannan ka'idoji a kai a kai. Ci gaba da amfani da bbc.co.uk tamkar ka amince da ka'idojin da aka yi wa sauye sauye ne. Idan ba ka amince da sauye - Sauyen da aka yi ba, to ka dakatar da mafani da shafin. Idan da akwai sabani tsakanin wadannan ka'idoji da kuma wasu ka'idojin dake cikin wani shafin na bbc.co.uk a yankin da kake, to dokokin yankin da kake su ne a gaba.