Abubuwa tara da suka ɗauki hankalin arewacin Najeriya a 2024
- Marubuci, Nabeela Mukhtar Uba
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Broadcast Journalist
- Twitter,
Al'amura da dama sun faru a shekarar 2024 da suka ɗauki hankalin mutane musamman a arewacin Najeriya kama daga fagen siyasa, da tattalin arziki, da zamantakewa har ma da batun tsaro.
A iya cewa 2024, za ta zama shekarar da zai yi wuya a iya mantawa da ita a arewacin Najeriya la'akari da yadda abubuwan da suka faru suka shafi rayuwarsu kai tsaye har ma a ka yi ta tafka muhawara a kai a shafukan sada zumunta.
A wannan maƙala, mun tattaro maku muhimman abubuwan da suka faru da suka ja hankalin arewacin Najeriya.
Ƙudirin Dokar Haraji
Wannan ne batu na baya-bayan nan da ya janyo cece-kuce da ya fuskanci adawa daga ɓangarori daban-daban na arewacin Najeriya.
Zuwa yanzu dai ƙudirin ya tsallake karatu na biyu a majalisar dattawa duk da cewa an tafka muhawara a zauren kafin a kai ga matakin.
Gwamnonin yankin Arewa sun yi adawa da ƙudirin saboda zargin da suka yi cewa tsarin zai ƙara dagula lissafin tattalin arzikin yankin.
Duk da adawar, gwamnatin Najeriya ta musanta zargin cewa ta ɓullo da tsarin ne domin dankwafar da wani yanki na Najeriya inda take cewa matakin zai buɗe sabbin hanyoyin tattara kuɗaɗen haraji domin amfanuwar ƴan ƙasa.
A halin da ake ciki dai an dakatar da muhawara game da ƙudirin a majalisar dattawa har sai an ji daga kwamitin da aka kafa domin ya sake tuntuɓa da kuma gyara ɓangarorin da ke janyo taƙaddama.
Katsewar lantarki
A iya cewa rashin lantarki ya zama jiki ga duk wani ɗan Najeriya sai dai a 2024 ne aka wayi gari gaba ɗaya yankin arewacin Najeriya ya faɗa cikin duhu.
Yanayin ya zo a daidai lokacin da ƙasar ke cikin halin matsi sakamakon tsadar man fetur.
An kwashe kwana 10 babu hasken wuta a yankin da ta samo asali bayan ɗaukewar wuta sau uku cikin kwana biyu sakamakon matsala daga babban layin wuta na Najeriya.
Lamarin dai ya jefa harkokin rayuwa da na tattalin arziki cikin mummunan yanayi inda aka tafka asara mara misaltuwa ta kayan abinci da sauran muhimman kayayyaki na miliyoyin kuɗi.
An kuma samu asarar rai a asibitoci sakamakon matsalar ta katsewar lantarki.
Zanga-zangar tsadar rayuwa da bayyana jagororinta
Zanga-zangar da aka yi tsakanin 1 zuwa 10 ga watan Agusta ta ja hankalin al'ummar Najeriya musamman yadda ta rikiɗe a arewacin ƙasar.
Tarzomar da aka tsara ta lumana ta zama tashin hankali a yankunan arewacin Najeriya ganin yadda aka riƙa ƙone-ƙone da yadda wasu ɓata-gari suka shiga cikin masu zanga-zangar.
Lamarin ya janyo hatsaniya da ruɗani har ma aka kai ga sanya dokar taƙaita zirga-zirga domin daƙile tarzomar a wasu jihohin arewa. An kuma kama mutanen da ake zargi da shirya-zanga-zangar.
Sai dai gabatar da mutanen gaban wata kotu a Abuja, babban birnin ƙasar bayan shafe kusan wata uku a tsare ya ɗauki hankalin jama'a ganin yadda suka bayyana a galabaice.
Hakan ya sa ɓangarori da dama ciki har da ƙungiyar Amnesty mai kare haƙƙin bil adama suka sa ƙaimi wajen kiran hukumomi su saki yaran.
Daga bisani shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya amsa kiran inda ya ba da umarnin sakin yaran tare da korar tuhumar da ake masu ta neman kifar da gwamnati.
Ambaliyar ruwan Maiduguri
Wani lamari da ya tada hankalin al'ummar arewacin Najeriya shi ne ambaliyar ruwan da ta faru a birnin Maiduguri na jihar Borno cikin watan Satumba.
Ibtila'in ya faru ne bayan fashewar madatsar ruwa ta Alau sakamakon tumbatsar da ta yi duk da cewa kafin nan, an yi ta jan hankalin hukumomi kan su ɗauki mataki.
Ambaliyar ruwan dai ta ɗaiɗaita mutum fiye da miliyan biyu baya ga rasa rayuka da kuma ɓacewar wasu a cikin ruwa.
Tsaga masarautu a arewacin Najeriya
A iya cewa wannan lamari na tsaga masarautu a arewacin Najeriya na neman zama gasa a tsakanin gwamnonin yankin.
A 2024, an samu jihohi da dama da suka saka batun yi wa masarautunsu garambawul cikin jadawalin ayyukan da suke son cimma.
A baya-bayan nan, gwamnatin Adamawa ta ɓullo da tsarin karɓa-karɓa a tsakanin shugabancin masarautun jihar abin da ke nufin muƙamin zai riƙa zagaya a tsakanin sarakunan jihar masu daraja ta ɗaya.
A Sokoto, majalisar dokokin jihar ta gyara dokar masarautun jihar inda ta rage wa Sarkin Musulmi ikon naɗa hakimai da dagatai.
Ko a Katsina ma, majalisar dokokin jihar ta amince da ƙudirin samar da dagatai takwas a masarautun Katsina da Daura.
Sake naɗa Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano
A cikin watan Mayun, 2024 ne Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya sanar da mayar da Muhammadu Sanusi II a matsayin sarkin Kano.
Haka nan gwamna Abba Kabir ya bayyana cewa a yanzu masarautar Kano ta koma matsayinta kafin yi wa dokar masarautar Kano gyaran fuska a 2019.
Sai dai hakan ya janyo rikici a masarautar kasancewar har yanzu Aminu Ado na zama a cikin birnin kuma ana ci gaba da jiran hukuncin kotun ɗaukaka ƙara bayan shari'o'in da kotunan ƙasa suka yanke.
Kisan Sarkin Gobir
Al'umma sun shiga cikin ɗimuwa da jin labarin kashe Sarkin Gobir da ƴanbindiga suka yi a watan Agusta.
Sarkin Gobir na Gatawa Isa Bawa ya shafe makonni a hannun ƴanbindigar inda har suka saki wani bidiyo da ya riƙa karakaina a shafukan sada zumunta da ke nuna marigayin yana neman taimakon hukumomi.
Kisan Sarkin ya fusata jama'a inda mutane suka yi ta bayyana fushinsu a shafukan sada zumunta.
Shugaban Najeriya ya yi tir da lamarin sai dai masana na ganin tashi tsaye ya kamata gwamnati ta yi wajen murƙushe ƴanbindigar da ke ƙara dagula lissafin tsaro.
Gobarar tankar mai a Jigawa
Hankalin al'ummar arewacin Najeriya ya yi matuƙar tashi da jin labarin fashewar wata tankar mai da ta halaka kusan mutum 200.
Lamarin ya faru ne sakamakon yadda mutanen yankin Majia suka yi dafifi wurin da tankar ta yi haɗari a ƙoƙarin su na kwasar man da ya malale a titi da sunan ganima.
Sai dai lamarin ya zo da tsautsayi inda tankar da kuma wuraren da man ya malale suka kama da wuta lamarin da ya shafi mutanen da ke wajen.
Sace ɗaliban Kuriga da gano su
A watan Maris ɗin 2024 ne ƴanbindiga suka kutsa ƙauyen Kuriga a jihar Kaduna inda suka yi awon gaba da ɗalibai 287.
A cikin watan Mayu ne kuma aka kuɓutar da ɗalibain inda bayan shafe kwana biyu a hannun gwamnati ana kula da lafiyarsu, aka miƙa su ga iyayensu.
Sai dai malamin da aka sace ɗaliban tare da su, ya rasa ransa a hannun ƴanbindigar.