Ƴan arewacin Najeriya shida da soshiyal midiya ta yi wa rana a 2024
- Marubuci, Nabeela Mukhtar Uba
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Broadcast Journalist
- Twitter,
Soshiyal midiya ta zama wata babbar kafa ta sauya rayuwar wasu ba zato ba tsammani kamar yadda Bahaushe ke cewa a dare ɗaya, Allah kan yi bature.
Haka lamarin yake ga wasu mutane da dama da za a iya cewa sun ci gajiyar kafar sada zumunta lamarin da ya daga likafarsu zuwa wani mataki a rayuwa.
Akwai mutane da dama da suka tsinci kansu cikin irin wannan yanayi kuma BBC ta zaƙulo shida daga cikinsu.
Hamdiyya Sidi Shariff
Labarin Hamdiyya Sidi Shariff ya taɓa mutane da dama ganin halin da ta tsinci kanta a ciki bayan da wani bidiyo da ta naɗa ya karaɗe shafukan sada zumunta.
A cikin bidiyon, Hamdiyya Shariff ta koka game da halin matsalar tsaro da al'ummar yankinta a jihar Sokoto suke ciki da kuma yadda ake cin zarafin mata.
Sai dai hakan ya sa gwamnati yi mata zargin ɓata sunan gwamna Ahmed Aliyu inda ta tsinci kanta a komar ƴansanda sai dai daga bisani ta shaƙi iskar ƴanci duk da cewa gwamnati ta musanta kama ta.
An kuma kai ta kotu aka kuma bayar da belinta.
Halin da ta tsinci kanta a ciki ya sa ƙungiyoyin lauyoyi da ƙungiyar Amnesty International suka soki gwamnatin jihar Sokoto tare da neman ta soke tuhume-tuhumen da take mata.
Lauyoyi kamar Audu Bulama Bukarti sun yi tayin tsaya mata domin kare kanta a kotu.
Ta kuma samu gurbin aiki a gidan rediyon Brekete Family a inda ta bayyana ta bayar da labarin irin barazanar da ta fuskanta.
Idris Yunusa - Ɗan Madara
Ga dukkan mai bin kafar Tiktok a arewacin Najeriya na san ya ci karo da labarin Idris Yunusa Ɗan Madara, wanda a baya ya yi ta'amali da ƙwaya.
An fi sanin dan madara a Tiktok kafar da yake wallafa bidiyoyi na al'amuran rayuwarsa da yadda yake yawan nuna sha'awarsa ta zuwa ƙasa mai tsarki.
Sanadiyyar haka ne kuma ya samu albishir daga wata ƙungiya da ta ɗauki nauyin kai shi Saudiyya domin ya yi ibadar Umrah, wani mataki da bai yi tsammanin kai wa ba a rayuwarsa.
Ko da ya je Umrah, an ga yadda ya shiga masallacin Annabi Muhammad SAW babu takalmi a ƙafarsa kamar yadda ya yi alƙawarin yi tun lokacin da bai samu albishir ɗin ba.
Usaina Iliyasu - Matar Seaman Abbas
Labarin Usaina Iliyasu ƴar jihar Taraba ga duk wanda ya ji na san zuciyarsa ta karaya kasancewar ta bayyana a shirin Brekete Family game da tsare mijinta da a lokacin yake aikin sojan ruwa a Najeriya tsawon shekaru har ta kai ga ya samu matsalar ƙwaƙwalwa.
Ta bayyana irin gwagwarmaya da fadi-tashin da ta yi don ganin an saki mijinta amma hakan ba ta samu ba.
Labarinta ya karaɗe shafukan sada zumunta lamarin da ya kai ga masu ruwa da tsaki sun sa baki har aka saki mijinta sai dai hukumomin soji, bayan sakinsa, sun kuma sanar da korar shi daga aiki.
Amma kafin nan, Usaina ta samu gudummawa da tagomashi daga mutane da dama domin ta fara jari da kuma ci gaba da kula da lafiyar mijinta.
Umar Bush
Umar Bush mutumin da ake kallo a matsayin mai saurin hassala da fushi a bidiyoyinsa da ake gani a shafukan sada zumunta, ya rabauta da muƙamin mai ba da shawara kan harkokin nishaɗii ga babban mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan masu buƙata ta musamman.
Mutane da dama sun soki muƙamin ganin yadda ake kallon shi a matsayin mai rangwamin hankali.
Ya kuma sami damar haɗuwa da manyan mutane a Najeriya da kuma samun kyaututtuka daban-daban.
Ya kuma zama ɗaya daga cikin abokan sana'ar ƴan wasan barkwanci daga kudancin Najeriya irin su Cute Abiola.
Fatima Mai Zogale
Sanadiyyar waƙar da shahararren mawaƙi Dauda Kahutu Rarara ya yi wa Fatima mai sana'ar sayar da zogale a Abuja, babban birnin Najeriya, matashiyar ta gamu da goma ta arziki daga mutane daban-daban.
Rarara ya ce maƙasudin wake Fatima mai zogale shi ne yadda ya yaba da daɗin zogalen da ya ci.
Wani abu da ya ƙara daukan hankalin mutane game da Fatima Mai Zogale shi ne yadda uwar ɗakinta ta kore ta bayan waƙar da Rarara ya yi mata.
Korar ce kuma ta sa mutane suka tausaya mata har ma ta samu gudummawa sosai, shi ma Rarara ya tallafa mata da jarin bunƙasa sana'arta ta sayar da zogale.
Aisha Ibrahim
Aisha Ibrahim mai sana'ar dafa abinci ce a jihar Bauchi da ta fito intanet tana kokawa da yaudarar da wani ya yi mata na ba ta kwangilar dafa abincin mutum sama da 9,600.
Ta ce ta kashe kusan naira miliyan 13 wajen dafa abinci kala-kala kamar yadda mutumin ya nema.
A cewarta, ta karɓo rancen kuɗaɗen ne da niyyar biyansu idan wanda ya ba ta kwangilar ya sallame ta.
Sai dai ta koka kan yadda mutumin da ya ba ta kwangilar ya ƙi ɗaga wayarta bayan ta gama aikin dafa abincin.
Fitowarta shafukan sada zumunta tana neman ɗaukin masu kuɗi da su sayi abincin da ta riga ta dafa don yin sadaka don gudun ka da su lalace ya sa mutane tausaya mata inda aka yi ta yaɗa bidiyon har gwamnatin jihar Bauchi ta kai mata ɗauki.
Gwamnatin jihar ta ba ta tallafin naira miliyan 7.5 tare da bayar da umarnin a gaggauta raba abincin ga mabuƙata.