Lokuta 10 da jiragen yaƙin Najeriya suka kai harin 'kuskure' kan fararen hula
Watanni 12 kenan cif-cif tun bayan da wani jirgin yaƙin Najeriya ya yi aman wuta bisa kuskure kan farar hula da ke taron Mauludi a ƙauyen Tudun Biri da ke jihar Kaduna, sai a gashi a ranar Larabar nan wani jirgin yaƙin ƙasar ya kuma kai irin wancan hari bisa kuskure a garin Silame na jihar Sokoto, al'amarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 10 sannan da dama sun jikkata.
Tuni dai hedikwatar tsaron Najeriya ta fitar da sanarwa tana cewa al'amarin ya faru ne bisa kuskure, a ƙaƙarinsu na kai wa ƴanta'adda hari a yankin.
Masana harkokin tsaro sun daɗe suna sukar irin sakacin da ake samu a yaƙi da ƴan Boko Haram a arewa maso gabas da kuma na 'yan ta-da-ƙayar-baya galibi a arewa maso yamma, da ke ritsawa da rayukan fararen hula wadanda ba su ji ba, ba su gani ba.
Ga jerin hare-haren da sojojin Najeriyan suka kai bisa kuskure a ƙasar:
1) - Silame - Jihar Sokoto, 25 Disamba 2024
Hare-haren da sojojin Najeriya na sama da na ƙasa suka kai a wasu ƙauyuka da ke jihar Sokoto sun yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutum 10 da raunata wasu da dama.
Lamarin ya faru ne da safiyar Laraba, yayin da jami'an sojin suka kai hari kan ƙauyukan, kamar yadda shugaban ƙaramar hukumar ya tabbatar wa BBC.
A tattaunawarsa da BBC, Abubakar Muhammad ya ce "Tun da safe aka kira ni aka shaida min cewa an ji saukar bama-bamai, inda na bincika na tabbatar da faruwar hakan."
Shugaban ƙaramar hukumar, wanda ya bayyana cewa shi da gwamnan jihar, Ahmad Aliyu na daga cikin waɗanda suka yi jana'izar mutanen da suka rasa rayukansu a lokacin harin, ya ce "jirgin yaƙi guda biyu ne suka saki bama-bamai" a kan ƙauyukan.
Ya ƙara da cewa "Sojojin sama ne da na ƙasa suka kai harin, sojojin sama sun shiga yankin da manyan tankokin yaƙi."
Shugaban ƙaramar hukumar ya ce baya ga mutum 10 da suka mutu, akwai kuma mutum shida da suka samu raunuka.
2) - Tudun Biri - Jihar Kaduna, 3 Disamba 2023
Hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Kaduna ta tabbatar da mutuwar mutum 85 a wannan hari da jirgi maras matuƙi na rundunar sojin ƙasa ya kai kan cincirindon mutane.
Sun taru ne don bikin Mauludi kamar yadda suka saba, a cewar wani mazaunin yankin, kuma malami a makarantar Madrasatul Madinatul Ahbab wa Talamiz, Bello Shehu Ugara, amma cikin dare sai jirgin sama ya je ya jefa musu bam.
"Mun kuma je, muna son mu tsame wa'inda ba su cika ba, da ke neman taimako, to an fara jawo wa'inda suke da sauran rayuwa, kuma jirgin again ya kuma dawowa ya jefa bam din."
Ya ce cikin wadanda suka mutu, akwai mata da ƙananan yara har da na-goye.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya mika sakon ta'aziyya ga dangin wadanda suka mutu, kuma ya ba da umarnin gudanar da cikakken bincike.
3) - Buhari - jihar Yobe, 15 Satumba 2021
Rundunar sojin saman Najeriya ta ce bisa kuskure jirgin sojinta ya kai hari tare da kashe fararen hula a garin Buhari da ke ƙaramar hukumar Yunusarin jihar Yobe a arewa maso gabashin Najeriya.
Shaidu sun ce harin jirgin saman na ranar Laraba ya kashe aƙalla mutum goma, baya ga gommai da suka jikkata, cikinsu har da mata da ƙananan yara.
Da farko dai rundunar sojin ta musanta faruwar lamarin, amma washe gari a ranar Alhamis ta fitar da wata sanarwa tana bayyana kuskuren da ya faru har aka samu aukuwar lamarin.
Ta ce jiragen sojin na shawagi ne a yankin Kogin Kamadougou na jihar Yobe, don tattara bayanan sirri a kan ƙungiyoyin Boko Hraam da ISWAP.
"Rundunar Operation Hadin Kai ta samu bayanan cewa ana aikata ayyukan ta'addanci a kan iyakar Najeriya da Nijar da misalin ƙarfe 6 na safe".
"A yayin da jirgin yake aiki a Kudancin Kanama sai ya gano wani shigi da ficen da bai yarda da shi ba mai alaƙa da ayyukan 'yan ta'addan Boko Haram.
"Daga nan, sai matuƙin jirgin ya bude wuta. Amma yana da muhimmanci a gane cewa da ma yankin ya yi ƙaurin suna da ayyukan Boko Haram da ISWAP."
Ta ce ta kafa kwamitin bincike kan abin da ya haddasa lamarin.
4) - Rann - jihar Borno, 18 Janairu 2017
Jami'an ba da agaji sun ce mutum 115 aka kashe a harin da jirgin yaƙin Najeriya ya kai, bisa kuskure a kan sansanin 'yan gudun hijira na Rann cikin jihar Borno.
Rundunar sojin Najeriya ta bayyana takaici dangane da lamarin, inda ta ce tuni ta fara gudanar da cikakken bincike.
Tun da farko, wani jami'i a jihar Borno, ya shaida wa BBC cewa mutum 236 ne suka mutu, kuma an yi jana'izarsu a ƙauyen na Rann.
Amma daga bisani shugaban ƙaramar hukumar ta Kala-Balge ya ce mutum 115 ne lamarin ya ritsa da su, yana mai cewa mutanen ƙauyen ne suka yi kuskure wajen bayyana adadin.
Ita dai, rundunar sojin Najeriya ta ce jirgin yaƙin ya kai hari kan mutanen bisa zaton cewa 'yan ƙungiyar Boko Haram ne.
Kungiyar ba da agaji ta Red Cross mai bayar da agaji ta ce harin ya yi matukar dimauta ta, tana mai cewa "irin wannan kuskuren abu ne da ba za a taba amicewa da shi ba."
Mutanen da luguden bama-bamai na Rann ya shafa dai, 'yan gudun hijira ne da ke tsere wa rikicin Boko Haram, wanda ya tagayyara rayuwarsu.
5) - Doma - jihar Nasarawa, 27 Janairu 2023
Wani ƙazamin harin jirgin sama ya yi sanadin kashe fararen hula aƙalla 28, a ƙauyen Rukubu na ƙaramar hukumar Doma cikin jihar Nasarawa da ke kan iyaka da jihar Binuwai.
Lamarin ya faru ne bayan makiyaya sun karɓi shanu daga hannun hukumomin Binuwai, tare da baro jihar domin zuwa wani wurin na daban.
Rahotanni sun ambato cewa tun da farko sojoji sun samu bayanan cewa akwai wasu da ake zargin ƴan ta-da-ƙayar-baya ne sun kutsa cikin wani yanki da ke iyakar Nasarawa da Binuwai.
Daga nan ne aka shirya samame na musamman domin yaƙar ƴan ta-da-ƙayar-baya, amma aka yi rashin sa'a aka far wa makiyayan da suka je belin shanunsu.
Ƴan sanda sun tabbatar da cewa mutum 28 ne aka yi jana'izarsu sakamakon harin.
Jaridun Najeriya dai sun ruwaito adadin da ya wuce haka, inda ko jaridar Punch ta ambato Gwamna Abdullahi Sule yana cewa aƙalla mutum 37 aka binne.
6) - Kwatar Daban Masara - Jihar Borno, 28 Satumba 2021
Fararen hula da dama ne suka mutu bayan hare-haren bam na jiragen yaƙi da ta yi nufin kai wa mayaƙan Iswap a ƙauyen Kwatar Daban Masara cikin yankin Tafkin Chadi ranar 28 ga watan Satumban 2021.
Kamfanin dillancin labarai na AFP a lokacin ya ce aƙalla masunta 20 aka kashe, amma a wasu bayanan sirri da BBC ta gani, rundunar sojin sama ta yi iƙirarin cewa masunci daya ne kawai ya mutu sai ƙarin shida da suka jikkata.
Sai dai wasu rahotanni sun ce mutum 50 zuwa 60 ne suka mutu a harin.
Tafkin Chadi, yanki ne da ya yi ƙaurin suna a yaƙin da Najeriya ke yi tsawon sama da shekara goma da mayaƙan Boko Haram, kuma a lokuta da yawa fada tsakanin sojoji da 'yan ta-da-ƙayar-bayan na ritsawa da fararen hula.
Daga bisani dai, Shalkwatar Tsaro ta fitar da sanarwa, inda ta dage a kan cewa luguden wuta da ta yi, ta yi su ne a kan wani sansanin mayaƙan Iswap da jami'anta suka shaida, amma ba masunta ba kamar yadda aka ba da rahotanni.
7) - Mainok - Jihar Borno, 25 Afirilun 2021
Wani harin jirgin saman sojojin Najeriya, ya hallaka sojin ƙasa da dama a wani farmaki da ya kai a garin Mainok mai nisan kilomita 55 daga Maiduguri.
Ko da yake, hukumomi a lokacin ba su bayyana adadin sojojin da aka kashe ba, amma wasu majiyoyin tsaro sun shaida wa BBC cewa kusan sojoji 30 ne suka mutu a luguden wutan.
Daga bisani, rundunar sojin sama ta bayyana cewa tana gudanar da bincike kan wasu hotuna da bidiyon da ake watsawa game da lamarin.
Rahotanni a lokacin sun nuna cewa an kashe sojojin ne yayin wani hari da mayaƙan Iswap suka kai kan sansanin dakarun sojin Najeriya da ke yankin, kuma jiragen sojin sama suka mayar da martani ta hanyar yin luguden wuta lokacin da suka je kai dauki don taimaka wa sojin ƙasa.
Mazauna garin da dama a lokacin sun shaida wa BBC cewa mayaƙan Boko Haram sun kashe fararen hula da dama a harin da suka kai, ciki har da wani malamin firamare da suka datse wa kai.
8) - Mutumji - Jihar Zamfara, 19 Disamba 2022
A Zamfara ma, daya daga cikin jihohin da ke fama da rikicin 'yan fashin daji a arewa maso yamma, jirgin yaƙi ya kashe aƙalla mutum 64 a wani luguden wuta da ya yi ranar Laraba a ƙauyen Mutumji cikin ƙaramar hukumar Maru.
Mazauna yankin a lokacin sun shaida wa manema labarai cewa an kuma kashe ‘yan ta-da-ƙayar-baya da yawa, ko da yake an ritsa da fararen hula mazauna garin ciki har da ƙananan yara.
Haka kuma an jikkata mutum 12 a harin bisa kuskure.
Mazauna yankin sun tabbatar da cewa samamen sojin sama a ƙauyuka uku masu makwabtaka, ya tilasta wa ‘yan ta-da-ƙayar-baya tserewa zuwa Mutumji da ke kusa don neman mafaka.
Gwamnatin tarayya a ranar 21 ga watan Disamba, ta fitar da sanarwa inda ta yi ƙarin haske a kan harin bayan taron majalisar zartarwa, ministan labarai na wancan lokaci, Alhaji Lai Mohammed ya bayyana harin da cewa abin takaici ne kuma sun yi nadamar faruwarsa.
9) - Kunkuman Bayan Dutse - jihar Katsina, 7 Yulin 2022
A jihar Katsina ma, an taba kai irin wannan hari a cikin watan Yulin 2022, inda aƙalla farar hula daya ya mutu, karin wasu 14 suka jikkata.
Lamarin ya faru ne a wani hari da jirgin saman sojin Najeriya ya kai da nufin far wa 'yan fashin daji da suka addabi yankin ƙaramar hukumar Safana.
Sai dai lamarin wanda ya faru ranar Talata da dare, ya bar ayoyin tambayoyi a zukatan jama'ar ƙauyen KunkuMan Bayan Dutse, wadanda bayanansu ya riƙa cin karo da na rundunar sojin ƙasar game da luguden bam din.
A yayin da mazauna ƙauyen ke cewa jirgin sojin Najeriya ne ya jefa musu bam wajen neman mafakar ƴan bindiga, rundunar sojan ta yi iƙirari cewa, dakarunta sun halaka 'yan ta-da-ƙayar-baya 24 ne kawai a harin da ta kai.
10) Nachade - Jamhuriyyar Nijar, 20 Fabrairu 2022
A wani ɓangaren kuma, sojojin Najeriya sun yi kuskuren kashe yara bakwai tare da jikkata wasu biyar a wani harin sama da suka kai a yankin Maradi na Jamhuriyyar Nijar, kamar yadda gwamman yankin ya shaida wa kamfanin dillacin labaran Faransa.
Gwamnan Maradi Chaibou Aboubacar, ya ce hare-haren sama, da sojojin Najeriya suka kai sun ritsa da yara a ƙauyen Nachade ranar Juma’a.
Gwamnan ya ce suna tunanin sojojin Najeriya sun yi kuskuren jefa wa yaran bam ne a ƙoƙarin kai hari ga ‘yan bindiga da ke tsallaka kan iyakar ƙasashen biyu suna kai hare-hare.
Gwamnan Maradi ya ce lamarin ya shafi yara ne guda 12, kuma bakwai daga cikin sun mutu, yayin da biyar suka jikkata.
A cewar gwamnan, harin ya ritsa da yaran ne suna cikin wasa yayin da iyayensu ke hidimar biki.