Isa ga babban shafi

Marine Le Pen ta gurfana gaban kotu kan badaƙalar kuɗaɗen majalisar EU

Jagorar jam’iyyar masu tsattsauran ra’ayi a Faransa Marine Le Pen ta gurfana gaban kotu ta musamman a yau Litinin don fara fuskantar tuhuma kan zargin amfani da kudaɗen ƙungiyar tarayyar Turai ta hanyar da bata kamata ba, a lokacin da ta jagoranci Majalisar ta EU.

Shugabar jam'iyyar masu tsattsauran ra'ayi ta Faransa Marine Le Pen.
Shugabar jam'iyyar masu tsattsauran ra'ayi ta Faransa Marine Le Pen. © Thomas Padilla / AP
Talla

Tun bayan fara fuskantar wannan tuhuma kusan shekaru goma da suka gabata, Le Pen tsohuwar ƴar takarar shugabancin ƙasa a Faransa da muƙarrabata 24 baya ga ita kanta jam’iyyar ta NR ko kuma National Rally za su amsa tuhumar ta karkatar da kudaden tafiyar da majalisar Turai zuwa tafiyar da jam’iyyarsu ta masu tsattsauran ra’ayi, ciki har da biyan wasu mambobin jam’iyyar albashi da kuɗin tafiyar da majalisar.

Tuni dai Marine Le Pen a jawabin da ta gabatar gaban manema labarai ta bayyana cewa ba ta shakkar wannan shari’a domin bata aikata wani laifi ba, a zargin na kashe tsabar kuɗin majalisar Turai da yawansu ya kai yuro miliyan 3.5 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 3.92.

Idan har ya tabbata Le Pen ta aikata laifukan da ake tuhumarta, kai tsaye za ta fuskanci haramcin aiki a ƙarƙashin wani ofishin gwamnati baya ga mummunan naƙasu ga tafiyar siyasarta.

Sai dai idan ƴar siyasar ta samu nasara a shari’a, hakan zai ƙarfafa mata gwiwar tunƙarar zaɓen shekarar 2027, musamman ganin yadda a yanzu haka ta ke da rinjayen mambobi a zauren majalisar Faransar.

A jawabin da ta gabatar, Marine Le Pen ta bayyana cewa makamantan shari’ar ba komai za su haifar ba face ƙara mata karsashi da magoya baya, kwatankwacin dai yadda ya ke faruwa da Donald Trump na Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.