Isa ga babban shafi

Venezuela ta zargi Amurka da shirya munaƙisar kashe shugaba Maduro

Gwamnatin Venezuela ta ce ta tsare wasu Amurkawa 3 da ta ke zargi da kitsa yi wa shugaba Nicolas Maduro kisan gilla, tana kuma zargin su da yi wa ƙasar zagon ƙasa.

Shugaban Venezuela Nicolas Maduro.
Shugaban Venezuela Nicolas Maduro. AP - Ariana Cubillos
Talla

A wannan Asabar, ministan cikin gidan Venezuela,  Diosdado Cabello ya sanar da cewa Amurkawa 3, ƴan ƙasar Spain 2 da wani ɗan kasar Czech ne su ka shiga hannu sakamakon shirin da ake zargin su na yi don hargitsa gwamnatin Maduro ta wajen tada husuma; ya kuma ƙara da cewa an karɓe ɗaruruwan makamai daga hannunsu.

Cabello bai bayyana ko su wanene waɗannan mutane da aka kama ba, amma ya yi ikiarin cewa hukumar leƙen asirin Amurka CIA, da CNI na Spain ne suka ɗauki nauyin shirya aika-aika. Ya kuma zargi jagorar  ƴan adawa, Maria Corina Machado daa hannu a shirya wa ƙasar munaƙisa.

Amurka ta mayar da martani ta ma’aikatar harkokin wajenta, inda ta bayyana a wata sanarwa cewa duk wani ikirarin tana da hannu a wata kutunguila da ake shirya wa Venezuela karya ce.

Sai dai ta tabbatar da cewa wai jami’in sojin Amurka na hannun mahukuntan Venezuela. Ta kuma ce akwai rahotannin da ba a tabbatar, waɗanda ke cewa ƙarin Amurkawa na tsare a ƙasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.