Isa ga babban shafi

Ya zama dole a tilasta wa Rasha hawa teburin sulhu - Zelensky

Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelenskiy  ya shaida wa kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya cewa ba zai yiwu a kawo ƙarshen yaƙin da ƙasarsa ke gwabzawa da Rasha ta maganar fatar baki ba kawai, don haka dole ne a tilasta wa Rashar don a samu zaman lafiya.

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky.
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky. AP - Christoph Soeder
Talla

Zelenskiy ya nemi goyon bayan jagororin ƙasashen yammacin Turai a kan abin da ya kira, ‘Shirin Nasara’ na kawo karshen yakin da ya ɓarke tun bayan da Rasha ta ƙaddamar da cikakkiyar mamaya a Ukraine a watan Fabrairun shekarar 2022.

Zelenskiy  ya ce lallai wata rana wannan yaki zai zo ƙarshe, amma ba domin wani ya gaji da yaƙin ba, ko kuma ta wajen cimma yarjejeniya da shugaba Vladimir Putin,  ya na mai nuni da tayin da aka yi wa ƙasarsa na yin haƙuri da yankunan da Rasha ta riga ta karɓe don warware rikicin.

Shugaban na Ukraien ya caccaki Korea ta Arewa da  Iran sakamakon taimaka wa Rasha da makamai da su ke yi, yana mai bayyana su a matsayin masu haɗin baki.

Ukraine na fuskantar makoma mai cike da rashin tabbas. Idan tsohon shugaba Donald Trump ya samu nasara a kan Kamala Harris a zaɓen shugaban Amurka na ranar 5 ga watan Nuwamba, manufofin Amurka a kan Ukraine na iya sauyawa, kuma hakan na iya shafar gudumawar kayan yaƙi da Ukraine ke samu a gun Amurka. Ƙuri’ar jin ra’ayin jama’a ya nuna cewa har yanzu babu wanda za a ce zai lashe zaɓen kai tsaye.

Sama da shekaru 2 da rabi da mamayar da Rasha ta fara a Ukraine, kash 20 na yankin Ukraine na hannun Rasha, kuma tana ci gaba da kutsawa ta gabashin ƙasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.