Neymar ya jefa kwallaye uku a raga
Kungiyar AC Milan ita ce kungiyar tilo daga Italiya da ta samu rayuwa a gasar zakarun Turai bayan an tashi wasa tsakaninta da Ajax babu ci a San Siro. A karon farko Neymar na Brazil ya yi wa Barcelona ruwan kwallaye uku inda ya taimakawa kungiyar lallasa Celtic shi 6 da 1.
Wallafawa ranar:
Tuni Juventus ta fice gasar bayan ta sha kashi a hannun Galatasaray ta Turkiya ci 1-0 a birnin Istanbul.
Galatasaray ce ta samu nasarar tsallakewa a rukuninsu na B inda take bi wa Real Madrid da ke jagorancin Teburinsu.
Napoli ma an yi waje da ita ne duk da cewa ta samu maki daya da Arsenal da Borussia Dortmund.
A daren jiya laraba Napoli ta doke Arsenal ne ci 2 da 0 a rukuninsu na F yayin da Borussia Dortmund ta doke Marseille 2 da 1 a Faransa.
Duk da dai Arsenal ta sha da kyar ne amma wannan ne karo na 14 da kungiyar ke tsallakewa zuwa zagaye na biyu a jere a gasar zakarun Turai.
A karon farko Neymar na Brazil ya yi wa Barcelona ruwan kwallaye uku inda ya taimakawa kungiyar lallasa Celtic shi 6 da 1. Yanzu Neymar ya zira kwallaye 5 ne a wasanni 20 tun zuwansa Barcelona.
Schalke 04 ma ta tsallake zuwa zagaye na biyu bayan ta doke FC Basel ci 2 da 0, Schalke 04 ce ke bi ma Chelsea da ta jagoranci teburin rukuninsu.
A birnin London Chelsea ta doke Steaua Bucharest ta Romania ci 1-0. A Birnin Vienna kuma Austria Vienna ta lallasa Zenit St. Petersburg ta Rasha ci 4-1. Yayin da Atletico Madrid ta Spain da doke FC Porto ta Portugal ci 2 da 0
Kungiyoyin da suka tsallake wadanda suka jagoranci teburin rukuninsu sun hada da :
Manchester United (Ingila)
Real Madrid (Spain)
Paris Saint-Germain (Faransa)
Bayern Munich (Jamus)
Chelsea (Ingila)
Borussia Dortmund (Jamus)
Atletico Madrid (Spain)
Barcelona (Spain)
Wadanda suka tsallake a matsayi na biyu sun hada da :
Bayer Leverkusen (Jamus)
Galatasaray (Turkiya)
Olympiakos (Girka)
Manchester City (Ingila)
Schalke (Jamus)
Arsenal (Ingila)
Zenit St Petersburg (Rasha)
AC Milan (Italiya)
A ranar Litinin din makon gobe ne za’a hada kungiyoyin da zasu kara da juna a zagaye na biyu bayan kammala zangon farko a jiya Laraba.
Kungiyoyin da suka fito a rukuni daya ba zasu hadu da juna ba haka kuma kungiyoyin da suka fito a kasa daya ba zasu hadu ba a zagaye na biyu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu