Isa ga babban shafi

Yadda ta kaya a wasannin gasar zakarun Turai

A daran jiya ne aka ci gaba da fafatawa a gasar zakarun Turai, Borussia Dortmund ta yiwa Celtic dukan kawo wuka, bayan da ta zazzaga mata kwallaye 7-1, wacce ke zama nasara mafi girma da ta samu a gasar zakarun Turai.

Ƴan wasan Dortmund, bayan tashi daga wasansu da Celtic.
Ƴan wasan Dortmund, bayan tashi daga wasansu da Celtic. REUTERS - Leon Kuegeler
Talla

Ɗan wasan Dortmund Karim Adeyemi ya samu nasarar zura kwallaye 3 a raga tun kafin aje hutun rabin lokaci, lamarin da ya sake jefa mafarki Celtic na taka rawar gani a gasar Turai cikin garari.

Arsenal da PSG

A wasan da aka yi tsakanin Arsenal da PSG a filin wasa na Emirates kuwa, kwallaye da Kai Havertz da kuma Bukayo Saka suka jefa ƙungiyar ne ya bata nasararta ta farko a wannan sabuwar gasar Turai.

Ɗan wasan gaba na Arsenal Kai Havertz.
Ɗan wasan gaba na Arsenal Kai Havertz. REUTERS - Hannah McKay

Ƴan wasan na Mikel Arteta dai sun buga kunnen doki ne a wasansu na farko da Atalanta a babbar gasar Turai ta bana.

Da wannan nasara, a yanzu Gunners ta doka wasanni 9 ke nan a dukkanin gasar bana da ta yi, ba tare da  rashin nasara ba.

Barcalona da Young Boys

Barcelona ta sake farfadowa a gasar zakarun Turai, inda ta lallasa Young Boys da ci 5-0, bayan da ta sha kashi a hannun Monaco a wasan farko da ta yi a wannan gasa.

Ɗan wasan gaba na ƙungiyar Barcelona Robert Lewandowski.
Ɗan wasan gaba na ƙungiyar Barcelona Robert Lewandowski. REUTERS - Albert Gea

Ɗan wasan gaba na ƙungiyar Robert Lewandowski ne ya samu nasarar jefa kwallo biyu a raga a wasan, wanda hakan ya sanya Young Boys komawa mataki na ƙarshe a teburin gasar, ganin yadda a wasan farko Aston Villa ta lallasasu a gida.

Leverkusen da AC Milan

Kwallo daya da tilo da Victor Boniface ya sanyawa Bayer Leverkusen, ya bata nasara akan AC Milan, wani lamari da ke kara fito da irin kokarin da ƙungiyar ke yi a gasar zakarun Turai.

AC Milan ta da taba lashe gasar karo biyar a tarihi, birinta ya shiga buhu ganin yadda tayi rashin nasara a dukkanin wasanni biyu da ta doka a gasar bana.

Inter Milan da Red Star

Ita kuwa Inter Milan a filin wasa na San Siro ta yi wa ƙungiyar Red Star Belgrade dukan wana kama, inda ta lallasa ta da ci 4 da nema.

Tun a mintuna na 11 da fara wasan ne dai Hakan Calhanoglu ya fara jefa kwallo a bugun tazara, kafin Mark Arnautovic ya kara ta biyu, sai kyaftin din ƙungiyar Lautaro Martinez ya jefa ta uku a minti na 71, sannan Mehdi Taremi ya ci ta 4 a bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Man City da Bratislava

Sai wasan da aka yi tsakanin Manchester City da Slovan Bratislava, City wacce ta buga kunnen doki a wasan farko da Inter Milan, a wannan karon ta dawo da ƙarfinta inda ta lallasa Slovan Bratislava da ci 4 da nema.

Ƴan wasan ƙungiyar Manchester City.
Ƴan wasan ƙungiyar Manchester City. REUTERS - David W Cerny

Ilkay Gundogan da Phil Foden suka jefa kwallaye biyu tun a mintuna 15 na farkon fara wasan, kafin Eirling Haaland da James McAtee suka kara.

Sauran sakamakon wasannin kuwa, RB Salzburg ta sha kashi ne a hannun Brest da ci 4 da nema, sai kuma VfB Stuttgart da Sparta Prague suka tashi 1-1.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.