EUFA ta caji CSKA Moscow akan koken Yaya Toure
Hukumar kwallon Turai ta EUFA ta caji kungiyar CSKA Moscow bayan zargin da Yaya Toure ya shigar an furta masa kalaman nuna wariyar launin Fata a wasan da Manchester City ta kai ziyara a Rasha.
Wallafawa ranar:
Yaya Toure yace abin bakin ciki ne bayan da magoya bayan CSKA Moscow suke ta yayata masa kalaman wariya da sunan Biri a lokacin da City ta doke CSKA ci 2-1.
Bayan shigar da koken da kungiyar Manchester City ta yi, hukumar kwallon Turai ta EUFA tace kwamitin ladabtarwarta zai yanke hukunci a ranar 30 ga watan Octoba.
Matsalar wariya dai matsala ce da bakaken fata ke fuskanta a Turai, irin haka ne ma yasa dan wasan Ghana Kevin-Prince Boateng, ya fice fili saboda kalaman wariya na sunan Biri da aka yayata masa a filin wasa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu