Isa ga babban shafi
Faransa-Ukraine

Faransa da Amurka sun gargadi Rasha kan mamaye Ukraine

Shugabannin kasashen Faransa da Amurka sun nemi Rasha ta taimaka wajen hana yaduwar tashe tashen hankulan da ke faruwa a Ukraine, ko kuwa manyan kasashen na duniya su dauki tsauraran matakai. Shugaban Faransa Francois Hollande, daya gana da shugaban Amurka Barak Obama ta wayar tarho, ya yi kira ga hukumomin birnin Moscow, su gaggauta kira ga ‘yan awaren da ke dauke da makamai a gabshin Ukraine su dakatar da hare haren su.Kiran na zuwa ne bayan sabon shugaban Ukraine ya nemi a tsagaita wuta, kiran da kwamandan ‘yan tawayen ya yi fatali dashi.Sai dai duk da wannan gargadin, shugaban na Rasha Vladmir Putin, ya yi kira ga dakarun kasar dake tsakiyar kasar su ci gaba da zama a cikin shirin ko-ta-kwana.Sanarwar, da ministan tsaron kasar Sergei Shoigu ya bayar, na zuwa ne kwana 1 kawai bayan da hukumomin na birnin Kremlin suka ce suna kara yawan sojojin Rasha a kan iyakarta da Ukraine. 

Shugaban Faransa, François Hollande da takwaranshi na Amurka, Barack Obama
Shugaban Faransa, François Hollande da takwaranshi na Amurka, Barack Obama REUTERS/Pascal Rossignol
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.