Isa ga babban shafi

Jimmy Carter ya cika shekaru 100 a duniya

Rana 1 ga watan octoban shekara 1924 aka haifi mutumin da ke matukar sha’awar noma gujiya a tsaunin Plains dake birnin Georjiya inda ya cigaba da tarewa bayan cire hanun sa daga duk wani lamarin da ya shafi  siyasa a shekara 1981

Tsohon shugaban Amruka Jimmy Carter
Tsohon shugaban Amruka Jimmy Carter REUTERS - John Amis
Talla

Jimmy Carter wanda shi ne Shugaban Amruka daya tilo daya tsallaka siradin shekara dari 1 tchitchib a raye, ya kasance guda daga cikin mutanen da sukayi ruwa da tsaki wajan kirkira da cimma yarjejeniya Camp David wacce ta samar da zaman lafiya tsakanin Isra’ila da Masar a cikin shekara 1979.

An samu hanun Jimmy Carter dumu-dumu a bakar siyasar Amruka tsakanin ta da abokiyar gabar ta Iran musamman kan batun dakarun Amruka da Jamhuriya muslunci ta yi garkuwa dasu tsakanin 1979 zuwa 1980.

A shekara 1982 Jimmy Carter ya kirkiri Gidauniya sa kan batun cigaba da inganta kiwon lafiya da kuma nemo hanyoyin magance rigingimu da tashe tashen hankulla a sasan duniya, gidauniyar da a karshin ta ya samu kyautar Nobel ta zaman lafiya.

A yau mahaifar sa ta Georjiya ke bikin murna cikar sa shekaru 100 a raye, inda aka tsara gudanar da faretin jiragen soji gami da nishadi tareda manya manyan mawaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.