Isa ga babban shafi

Ina sane da halin ƙuncin da kuke ciki - Tinubu

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya amince cewa manufofin da gwamnatinsa ta zo da su ne suka kara ta’azzara halin ƙuncin da ake ciki a ƙasar, inda ya bai wa ƴan kasar tabbacin cewa gwamnatinsa ta maida hankali wajen warware matsalolin da suke ciki.

Shugaban Najeriya Bola Ahmaed Tinubu yayin bukin ranar Demokradiya.25/05/24
Shugaban Najeriya Bola Ahmaed Tinubu yayin bukin ranar Demokradiya.25/05/24 © Nigeria presidency
Talla

A cikin jawabin da ya yi wa ƴan ƙasar a wannan safiya na ciki shekaru 64 da samun ƴancin kai, Tinubu ya ce yana sane da matsalolin da al’ummar kasar ke ciki musamman na tsadar rayuwa da rashin aikinyi da dai sauransu.

Gwamnatinmu ta san cewa da yawa daga cikinku suna fama da tsadar rayuwa da kuma rashin aiki. Ina so in tabbatar muku cewa mun saurari sakonku.

Tinubu ya bukaci ƴan Najeriya su kara hakuri, domin acewarsa sauye-sauyen da suke gudanarwa sun fara haifar da ɗa mai ido.

Najeriya dai na fuskantar matsalar tsadar rayuwa mafi muni a tarihi, sakamakon cire tallafin man fetur da kuma faduwar darajar kudin Naira da aka samu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.