Isa ga babban shafi

Ana fargabar mutane 64 sun mutu sakamakon kifewar kwale-kwale a Zamfara

Akalla mutane 64 ne ake fargabar sun mutu biyo bayan wani hatsarin kwale-kwale a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya, kamar yadda mahukunta su ka bayyana a Asabar.

Kwale-kwale a kogin iyakar Nijar da Mali
Kwale-kwale a kogin iyakar Nijar da Mali AFP/François Xavier Marit
Talla

Wani kwale-kwalen katako mai ɗauke da mutane 70 ne ya kife a yayin da ya ke ƙoƙarin tsallakar da su zuwa gonakinsu a garin Gummi da safiyar Asabar.

Rahotanni sun ce ba tare da ɓata loaci ba mahukuntan yankin suka shirya aikin ceto, inda bayan laluɓe na tsawon sa’o’i 3, aka ceto mutane 6 daga kogin.

Sama da manoma ɗari 9 su ke tsallakawa wannan kogi kulayaumin don isa ga gonakinsu, amma kwale-kwale biyu ne kaɗai ake da su a wannan yankin, lamarin da ke haddasa ɗaukar fasinjoji fiye da kima, kamar yadda wani basaraken yankin ya bayyana.

Jihar Zamfara wanda ayyukan ƴan bindiga  daa ke neman iko da albarkatun ƙasa  ya yi wa katutu ta kuma fuskanci matsalar ambaliyar ruwa sakamakon mamamkon ruwan sama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.