Isa ga babban shafi

Buhari ya kafa kwamitin nazari kan yajin aikin ASUU

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kafa wani sabon kwamiti domin nazartar bukatun Kungiyar Malaman Jami’o’in kasar ta ASUU wadda ke ci gaba da yajin aikin sai-baba-ta-gani.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, 2022
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, 2022 © Bashir Ahmad
Talla

Ministan Ilimi Adamu Adamu da ya gana da shugabannin jami’o’in a birnin Abuja a wannan Talatar, shi ne ya sanar da matakin gwamnatin tarayya na kafa sabon kwamitin.

Kwamitin ya kunshi shugabannin gudanarwar jami’o’i hudu da kuma shugabannin jami’o’i uku, yayin da shi Ministan zai jagoranci kwamitin.

Babban aikin da ke gaban kwamitin shi ne, nazartar karin bukatun kungiyar ASUU, musamman ma a bangarorin da suka gaza cimma jituwa da gwamnati.

Sai dai Ministan ya ce, dole ne shugaban ASUU ya janye kalamansa na cewa, kungiyar ba za ta sake shiga duk wata yarjejeniya da gwamnatin Buhari ba.

Tun a cikin watan Fabairu ne dai, ASUU ta tsunduma yajin aiki, tana mai bukatar gwamnati da ta inganta jami’o’in kasar da kuma albashi da kudaden alawus-alawus na malamai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.