Isa ga babban shafi
Najeriya

Jibrin ya aika wasika don tuhumar Dogara a Najeriya

Tsohon shugaban kwamitin kula da kasafin kudi a majalisar wakilan Najeriya, Abdulmumin Jibrin ya ce, ya aike da wasika ga hukumomin yaki da cin hanci da rashawa don gudanar da bincike kan zargin da ya ke yi wa bangaren shugabancin Majalisar.

Kakakin majalisar wakilan Najeriya, Hon. Yakubu Dogara
Kakakin majalisar wakilan Najeriya, Hon. Yakubu Dogara bellanaija.com
Talla

A wani sako da ya aika a shafinsa na Twitter, Jibrin ya ce, an kara girke masa jami’an tsaro saboda yadda ya zama babban mai bayar da sheda kan binciken da kuma tuhumar kusoshin majalisar.

Mr. Jibrin na zargin shugaban majalisar Yakubu Dogara da mataimakinsa Yusuf Lasun da wasu kusoshin majalisar guda  biyu da cin amana da kuma yunkurin shigar da cuwa-cuwa a kasafin kudin shekarar 2016, lamarin da ya haifar da cece-kuce a duk fadin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.