Isa ga babban shafi
EU-Amurka-Najeriya

Farashin danyen mai ya tashi, Kasashen Turai da Amurka sun nuna damuwa

Farashin danyen mai a kasuwar duniya ya tashi a dai dai lokacin da kudin euro ke shan kashi hannun dalar Amurka wajen kokarin sabunta hanyoyin magance matsar bashin Turai. Farashin danyen man kasar Amurka ya tashi al’amarin da ke haifar da damuwa ga mabukata.

Matatar man Fetur ta kasar Iran.
Matatar man Fetur ta kasar Iran. REUTERS/Caren Firouz
Talla

Hakan kuwa na zuwa ne sanadiyar samun sabani tsakanin kasashen yammaci da kasar Iran daya daga cikin manyan kasashe masu samar da danyen mai. 'Yan kasuwa suna cin riba fiye da kima.

A wata fuska Farashin man yana fuskantar barazana da kalubale ne bisa fargabar da ake da ita ga matsalar tattalin arzikin Turai.

Yanzu haka Dalar Amurka na ci gaba karfafa tare da yin ruwa da tsaki ga farashin Mai bayan da kudin euro ya fadi zuwa $1.2777 mafi faduwa tun ranar 13 ga watan Satumba.

A ranar Laraba farashin Mai ya haura sama bayan da kungiyar kasashen Turai suka cim ma yarjejeniyar karfafa kakubawa kasar Iran Takunkumi.

Kamfanin hako Mai na Shell ya yi gargadin samun karancin Man bayan kai hari ga bututun mai a kudancin Najeriya inda za’a kwashe kwanaki kafin a gyara.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.