Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar 27 ga watan 12, 2024.

Rahoto kai-tsaye

Isiyaku Muhammad, Haruna Ibrahim Kakangi

  1. Kumbon da aka tura domin nazarin rana ba ya cikin barazana

    Kumbo

    Asalin hoton, NASA

    Kumbon masu bincike na Nasa wanda aka tura domin nazarin yadda rana ke aiki ya kafa tarihin zuwa kusa rana da ba a taɓa yi ba a baya ba.

    Masu binciken Nasa sun samu alama daga kumbun ne a daren Alhamis bayan kwanaki ba su ji daga gare shi.

    Masu binciken sun ce kumbun ya isa kuma ya yi shawagi lafiya ƙalau a kusa da rana bayan kusantar rana da tafiyar mita miliyan 3.8 (kimanin kilomita miliyan 6.1) daga

    Kumbun ya kutsa kusa da rana ne a yammacin jajibarin Kirsimeti duk da ƙarfin zafin da rana ke fitarwa,

    Kumbun da ya shanye zafin rana na kunsa 1,800 a ma'aunin faranheit, wanda ya yi daidai da kimanin zafin 980 a ma'aunin celcius.

    Dokta Nicola Fox, wanda shi ne shugaban masu binciken kimiyya na Nasa ya taɓa faɗa wa BBC cewa, "shekaru da dama da suka wuce mutane suna ta nazartar yanayin rana, amma babu wanda zai iya gane haƙiƙan yadda lamarin yake sai an je an gani."

  2. Mayakan Houthi sun ce za su ci gaba da kai wa Isra'ila hari

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    Wani babban kwamandan mayaƙan Houthi ya shaida wa BBC cewa za su ci gaba da kai wa Isra'ila hari duk da hare-haren da Isra'ila ta kai ta sama a ranar Alhamis da ya kashe mutum shida.

    Mohammed Al Bukhaiti ya ce kuma sun sa kafar wando guda da Amurka da kuma Birtaniya saboda goyon bayan da suke nuna wa abin da ya kira kisan kiyashin Isra'ila a Gaza.

    Al Bukhaiti ya ce yaƙin ya haɗa kan al'ummar Yemen kuma zai iya ruruwa idan aka rantsar da Trump.

  3. Amurka ta ce an kashe ɗaruruwan sojojin Koriya ta Arewa a yaƙin Ukraine

    Ana tunanin Koriya ta Arewa ta tura dakaru sama da 10,000 domin taimaka wa Rasha a yaƙin Ukraine

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Ana tunanin Koriya ta Arewa ta tura dakaru sama da 10,000 domin taimaka wa Rasha a yaƙin Ukraine

    Fadar White House ta ce sojojin Koriya ta Arewa kusan dubu ɗaya ne ko dai aka kashe ko kuma aka jikkata a makon da ya gabata bayan da suka tafi taimaka wa Rasa domin yaƙar sojojin Ukraine a yanin Kursk na Rasha.

    Kakakin ma'aikatar tsaron Amurka, John Kirby ya ce a bayyane take cewa shugabannin sojojin Rasha na kallonsu a matsayin marasa muhimmanci inda suke ba su umarnin kai hare-hare.

    Ana tunanin an tura kusan ƴan Koriya ta Arewa dubu goma sha biyu zuwa Rasha domin taimaka mata ta sake ƙwace iko da wasu yankunan Kursk da ta mamaye.

    Kalaman Mista Kirby sun yi daidai da binciken da jami'an sojin Koriya ta Kudu suka yi a farkon makon nan.

  4. Isra'ila ta tilasta kwashe marasa lafiya a asibitin arewacin Gaza

    Hotn

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Wasu Falasɗinawa kenan da ke neman 'yan'uwansu bayan harin Isra'ila ya faɗa kan asibiti ranar kirsimeti

    Rundunar sojin Isra'ila ta tilasta kwashe marasa lafiya a ɗaya daga cikin asibitocin da suka rage a arewacin Gaza inda ta kira shi a matsayin 'cibiyar ta'addancin Hamas'.

    Asibitin Kamal Adwan ya shafe makonni yana fuskantar hare-hare daga dakarun IDF.

    Lamarin ya faru ne bayan kashe mutum 50 ciki har da likitoci biyar a wasu jerin hare-hare da aka kai hamɓarar a asibitin cikin dare.

    Wani jami'i a asibitin ya shaida wa BBC cewa sojoji sun gargaɗe su da kwashe marasa lafiya da ma'aikata zuwa wani ɓangare na daban.

    Sojojin Isra'ila daga bisani sun kutsa cikin asibitin inda suka riƙa kwashe ragowar marasa lafiyar da ke ciki.

  5. Gwamnatin Sokoto ta ƙaddamar da rabon tallafi ga masu ƙaramin ƙarfi

    Gwaman Sokoto

    Asalin hoton, Ahmad Aliyu/X

    Gwamnatin jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya, ta ƙaddamar da shirin rabon tallafin kuɗi ga masu ƙaramin ƙarfi a jihar.

    Shirin - wanda gwamnan jihar, Ahmad Aliyu ya ƙaddamar ranar Juma'a a birnin Sokoto - na da aniyar tallafa wa masu ƙaramin ƙarfi domin rage talauci a cikin al'umma.

    Sokoto

    Asalin hoton, Sokoto State Government

    Yayin da yake jawabi a wajen ƙaddamar da shirin, Gwamna Ahmad Aliyu ya ce shirin na daga cikin jerin shirye-shiryen bayar da tallafi domin dogaro da kai da gwamnatinsa ta ɓullo da su.

    ''A yau ma za mu kafa sabon tarihi, inda za mu fara raba kuɗin tallafi domin dogaro da kai ga masu ƙaramin ƙarfi. Kimanin mutum 9,700 za su rabauta da wannan tallafi a wannan karo, inda wasu za su samu naira 75,000 wasu kuma naira 100,000 yayin da wasu samu samu naira 150,000'', in ji gwamnan.

    Gwamantin Sokoto

    Asalin hoton, Sokoto State Government

    Ya ƙara da cewa ''Mun bayar da wannan tallafi ne domin ƙarfafa wa jama'a gwiwa don fara sana'o'in dogaro da kai''.

    Haka kuma Gwamnan ya yi kira ga mutanen da suka amfana da tallafin da su yi amfani da kuɗin ta hanyar da ta dace, wajen kafa sana'o'in dogaro da kai domin su tallafi kawunansu.

    Sokoto

    Asalin hoton, Sokoto State Government

  6. An yi wa wani bulala 60 bayan keɓewa da wata mata

    Mutumin da aka yi wa bulala 60 a wani Masallacin Kuala Terengganu

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Mutumin da aka yi wa bulala 60 a wani Masallacin Kuala Terengganu

    An yi wa wani mutum bulala a cikin masallaci a Malaysia bayan ya keɓe tsawon lokaci da wata da ba matarsa ba ko ƴar'uwarsa.

    Wannan ne karon farko da aka zartar da irin wannan hukunci a Masallaci, maimakon kotun shari'a.

    Mutane da dama ne suka taru lokacin da ake zartar wa mutumin mai shekara 42 hukuncin bulala. Sai dai ba a san ko akwai wani hukuncin da aka zartar wa matar ba.

    A 2018, an taɓa yi wa wasu mata biyu bulala kan laifin aikata zina.

  7. Bama-baman Lakurawa ne suka kashe mutane a Silame ba harin sojoji ba - Sojoji

    soja

    Asalin hoton, Defence HQ/X

    Rundunar sojin Najeriya ta ce bama-baman da Lakurawa suka ajiye a ƙauyukan da sojojin suka kai wa hari ne suka kashe mutanen gari, ba hare-haren da sojojin suka ƙaddamar ba.

    A ranar Laraba da safe ne aka samu rahotonnin hare-haren jiragen sojin Najeriya a wasu ƙauyuka biyu da ke yankin ƙaramar hukumar Silame a jihar Sokoto.

    Gwamnan jihar, Ahmad Aliyu ya ce sojojin ƙasar ne suka kai harin bisa kuskure, lamarin ya yi sanadin mutuwar mutum 10, wani abu da gwamnan ya danganta da ƙaddara.

    To sai dai cikin wata sanarwa da shalkwatar tsaron ƙasar ta fitar mai ɗauke da sa hannun daraktan yaɗa labaranta, Manjo JanarEdwar Buba ya fitar ya ce ba harin sojojin ne ya kashe mutanen ba.

    Ya ce kafin kai harin, sai da sojojin suka ɗauki tsawon lokaci suna gudanar da cikakken bincike ta hanyar tattara bayanan sirri, sanna suka tabbatar da cewa Lakurawa ne ke karakainarsu a yankin.

    ''Sannan jirginmu ya ƙaddamar da hare-hare kan wuraren da muka tabbatar da cewa na Lakurawa ne da misalin ƙarfe 6:00 na asubahin ranar 25 ga watan Disamba, ta hanyar amfani da ƙananan makamai domin taƙaita ɓarnar da hare-haren za su haifar,'' in ji Manjo Janar Edwar Buba.

    sosjoji

    Asalin hoton, Defence HQ/X

    Bayanan hoto, Manjo Janar Edwar Buba

    Ya ƙara da cewa bayan harin dakarunsu da ke ƙasa sun je wurin domin tantance harin.

    ''Kuma sun tabbatar mana cewa hare-haren sun yi nasara, domin sun lalata maɓoyar Lakurawan, tare da 'yar ƙaramar ɓarna a ƙauyen. Haka kuma sojojinmu na ƙasa sun zanta da mutanen ƙauyen inda suka tabbatar musu cewa akwai Lakurawa a inda aka kai harin,'' in ji shi.

    Ya ci gaba da cewa hare-harenmu sun yi nasara wajen kashe Lakurawa a yankin tare da lalata muhimman abubuwan da Lakurawan ke amfani da su ciki har da makamansu.

    ''Don haka faɗawar harin kan rumbun makaman Lakuwarar ya haifar da wasu ƙarin fashe-fashen bom a wurare daban-daban, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 10, kuma muna kan bincike domin tabbatar da cewa ko suna cikin masu taimaka wa Lakurawan ko akasin haka,'' a cewar sojojin na Najeriya.

    Sanarwar ta ci gaba da cewa mutanen yankin sun tabbatar musu cewa Lakurawa na gudanar da harkokinsu a yankin.

  8. Mun ji ƙarar fashewa kafin jirginmu ya rikito - Fasinjoji

    Kazakhstan

    Asalin hoton, Reuters

    Wasu fasinjoji da suka tsira daga hatsarin jirgin sama a Kazakhstan, wanda ya yi ajalin aƙalla mutum 38 sun ce sun ji ƙarar fashewar wani abu kafin jirgin ya faɗi.

    Fasinja biyu, waɗanda yanzu haka suke asibiti, sun ce a lokacin da jirgin ke ya kusa sauka a garin da zai je a Chechnya a ranar Laraba ne wani abu mai ƙarfi ya fashe.

    Kamfani jirgin, wato Azerbaijan Airlines, ya ce jirgin ya samu rauni a jikinsa da kuma a ɓangaren na'ura, wanda ya jawo hatsarin.

    Tuni dai kamfanin ya sanar da dakatar da hada-hada zuwa wasu biranen Rasha.

  9. Kifewar jirgin ruwa ya yi ajalin aƙalla mutum 69 a Maroko

    Maroko

    Asalin hoton, Getty Images

    Aƙalla mutum 69, ciki har da ƴan ƙasar Mali 25 ne suka rasu bayan wani jirgin ruwa da ya taso daga Maroko zai tafi Spain ya kife a cikin teku.

    Hukumomin ƙasar sun tabbatar da cewa ƴan ƙasar na cikin fasinjoji 80 da suke jirgin, wanda mutum 11 ne kawai suka tsira, ciki har da ƴan Mali 11.

    Tun a makon jiya ne jirgin ya kife, amma sai jiya Alhamis aka samu tabbacin adadin waɗanda suka rasu.

    Wata ƙungiya mai suna Caminando Frontiers ta ce aƙalla mutum 10,000 ne suka rasu a cikin teku a yunƙurinsu na tsallakawa Spain daga ƙasashen Afirka a bana.

  10. Ku San Malamanku tare da Sheikh Ahmad Abdulkadir

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo

    A cikin shirinmu na Ku San Malamanku, a wannan makon mun kawo muku fira da Sheikh Ahmad Abdulƙadir.

    An haifi shehin malamin addinin Musulunci a unguwar Furemari da ke birnin Maiduguri a ranar 25 ga watan Yulin 1968.

    Malamin ya taso a hannun kakarsa a unguwar Yafateri, inda ya fara karatun allo a wajen Mariya Gwani Amma.

    Bayan ya yi sauka, ya shiga makarantar furamare a shekarar 1982, sannan ya zarce zuwa makarantar sakandare, ya kuma kammala digirinsa a fannin shari'a a Jami'ar Maiduguri, kafin ya je makarantar horas da lauyoyi.

    Sheikh Ahmad ya yi karatu a wurin manyan malamai da suka haɗa da Sheikh Abubakar Garba Ɗanyaya da Sheikh Sharu Abduljami da Sheikh Dakta Muhammad Kasim Muhammad da sauransu.

  11. Majalisar Koriya ta Kudu ta kaɗa ƙuri'ar tsige shugaban riƙo na ƙasar

    Koriya ta Kudu

    Asalin hoton, Getty Images

    Majalisar Koriya ta Kudu ta kaɗa ƙuri'ar tsige shugaban ƙasar na riƙo Han Duck-soo, kimanin mako biyu bayan tsige Shugaban Ƙasar Yoon Suk Yeol.

    Ƴan majalisa 192 ne suka kaɗa ƙuri'ar amincewa, bayan ta ce ana buƙatar aƙalla ƙuri'a 151 domin tsige shugaban.

    Ƴanmajalisar jam'iyyar PPP mai mulki sun nuna rashin jin daɗinsu bayan shugaban majalisar ya sanar Won-shik ya ce ana buƙatar aƙalla ƙuri'a 151 ne domin a tsige shugaban.

    Hakan na nufin, ba kamar ƙuri'a 200 da aka buƙata kafin tsige Yoon ba, yanzu ko da ƴan majalisar jam'iyya mai mulki ba su amince ba, ƙuri'ar ƴan hamayya kaɗai ta wadatar.

    Ƴan majalisar hamayyar sun fara yunƙurin tsige shugaban riƙon ne bayan ya ƙi amincewa da naɗa alƙalan da majalisar ta naɗa domin sauraron shari'ar Yoon.

    A dokar Koriya ta Kudu, kotun ƙasar mai alƙalai tara, ana buƙatar aƙalla alƙalai shida domin tabbatar da tsige Yoon.

    Yanzu alƙalai shida ne kawai a kotun, wanda hakan ke nufin idan alƙali ɗaya ya ƙi amincewa, tsigewar ba za ta yiwu ba, wanda hakan ya sa ƴan majalisar hamayya suke son ƙara alƙalai.

    Wannan ne karon farko da za a tsige shugaban riƙo a ƙasar, kuma ana sa ran ministan kuɗi, Choi Sang-mok zai yi riƙon ƙwaryar shugabancin ƙasar.

  12. Za mu yaƙi ƙudurin haraji na Tinubu - Gwamnan Bauchi

    Bauchi

    Asalin hoton, Bauchi State Government

    Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed ya yi kira ga Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da ya dakata da batun gyare-gyaren haraji da ya ɗauko.

    Ya bayyana haka ne a ranar Alhamis lokacin bikin Kirsimeti da ya shirya wa al'ummar Kirista a jihar.

    Ya ce ƙudurorin ba za su yi wa ƴan arewa kyau ba, inda ya ce gwamnoni ba za su iya biyan albashi ba.

    Ya ce, "ƙudurorin haraji ba za su amfani arewacin Najeriya ba. Dole su saurare mu, idan ba su saurare mu ba, ke nan an koma kama-karya, kuma hakan ba shi da kyau.

    "Bai kamata su yi ƙudurori da za su amfani jiha ɗaya ba kawai. Ba wai maganar addini ko ƙabilanci ake ba, magana ce ta haɗin kan ƙas," kamar yadda Channels ta ruwaito.

    Ya ƙara da cewa za su cigaba da matsa lamba domin a yi abin da ya dace, "amma idan suka ƙi, ba za su ƙi gani ba. Za mu yaƙi lamarin."

  13. 'Ukraine ta kama sojan Koriya ta Arewa da ke taya Rasha yaƙi'

    Ukraine

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar leƙen asirin Koriya ta Kudu ta ce sojojin Ukraine sun kama wani sojan Koriya ta Arewa da ke yaƙi tare da sojojin Rasha.

    Rahoton na ta ya yi daidai da wanda jaridar sojin Ukraine ta wallafa da ke cewa an kama sojan ne a wani samame da aka yi a birnin Kursk.

    Ana tunanin shi ne ɗan Koriya ta Arewa na farko da sojojin Ukraine suka kama daga cikin sojojin Koriya ta Arewa dubu goma da ake kyautata zaton suna taimakawa Rasha a yaƙin da take yi da Ukraine.

  14. Mali na neman ƴan ƙasarta 25 da suke cikin jirgin da ya nutse a hanyar Spain

    Gwamnatin Mali ta ce ƴan ƙasarta 25 na daga cikin ƴan ci-rani da dama da har yanzu ba a gansu ba bayan jirgin ruwan da suke ciki ya nutse a makon da ya gabata yayin da suke ƙoƙarin ƙetarawa zuwa ƙasar Spain.

    Sanarwar da kamfanin dillancin labaran Faransa ya bayar ta ce an ceto mutane goma sha ɗaya.

    Jirgin ruwan dai ya taso ne daga ƙasar Maroko ɗauke da fasinjoji kusan tamanin.

    A cewar wata ƙungiyar kare haƙƙin ɗan'adam a Spain, a wannan shekarar, fiye da mutum dubu goma ne suka mutu a yayin da suke ƙoƙarin zuwa Spain ta jirgin ruwa daga Afirka.

  15. Sojoji sun kashe ƙasurgumin ɗanbindiga Ma'oli a Zamfara

    CG Musa

    Asalin hoton, X/Defence HQ

    Sojojin birged na 1 na dakarun Operation Fansan Yamma, sun kashe wasu ƴanbindiga, ciki har da wani ƙasugumi, Alhaji Ma'oli, a ranar 26 ga Disamban 2024.

    Sojojin sun kai farmakin ne a ƙauyen Mai Sheka, kusa da garin Kunchin Kalgo, inda Ma'oli ya daɗa yana ƙuntata wa jama'a ta hanyar ƙaƙaba wa mazauna Unguwar Rogo da Mai Sheka da Magazawa da yankin Bilbis da ke ƙaramar hukumar Tsafe haraji.

    Kakakin jami'an tsaron haɗin gwiwar, Abubakar Abdullahi ya ce kashe Ma'oli ya jefa farin ciki a zukatan mutanen yankin.

    Sojojin sun kai farmakin ne bayan samun bayanan sirri kan harkokin ƴanbindiga a yankin Bilbis, wanda hakan ya sa sojojin suka kai ɗauki, suka samu nasarar ɗakile yunƙurin ƴanbindigar.

  16. Farfaganda ba za ta hana ni aiki ba - Wike

    Wike

    Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ce batun da ake yaɗawa cewa yana ƙwace filaye ba haka ba ne, inda ya ce yaƙi yake yi da masu ƙwace filaye, ba shi yake ƙwacen ba.

    Wike ya bayyana haka ne a ranar Alhamis a wani taron da ƴan PDP na ƙaramar hukumar Ahoada ta Gabas na jihar Ribers, inda ya yi godiya ga Shugaban Ƙasa Bola Tinubu bisa damar da ya ba shi, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

    Wike ya ce, "ina yaƙi ne da masu ƙwacen filaye. Wasu na cewa wai ƙwacen filaye ake yi, ta yaya za ka ƙwace filaye alhali kai ne ke da iko da filayen? ni nake da iko filaye a Abuja, to ta yaya zan ƙwace abun da nake da iko a kai?"

    Ya ƙara da cewa yanzu ba kamar Rivers ba, da ƴan Najeriya baki ɗaya yake aiki, wanda hakan ya sa ƙara fahimtar wasu abubuwa.

    "Wasu suna tunanin don ba a yi amfani da doka ba a baya, babu wanda zai zo ya yi. Amma ba haka ba ne, don wata gwamnati ba ta yi ba, hakan ba ya nufin babu gwamnatin ba za ta zo ta gyara. Don haka duk farfagandar da za a yi, ba za ta hana ni yin abubuwan da suka dace ba."

  17. Ku San Malamanku Tare da Sheikh Ahmad Abdulkadir

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon

    A cikin shirinmu na Ku San Malamanku, a wannan makon mun kawo muku fira da Sheikh Ahmad Abdulƙadir.

    An haifi shehin malamin addinin Musulunci a unguwar Furemari da ke birnin Maiduguri a ranar 25 ga watan Yulin 1968.

    Malamin ya taso a hannun kakarsa a unguwar Yafateri, inda ya fara karatun allo a wajen Mariya Gwani Amma.

    Bayan ya yi sauka, ya shiga makarantar furamare a shekarar 1982, sannan ya zarce zuwa makarantar sakandare, ya kuma kammala digirinsa a fannin shari'a a Jami'ar Maiduguri, kafin ya je makarantar horas da lauyoyi

  18. ECOWAS ta 'ƙaryata' zargin da Nijar ke yi wa Najeriya

    ECOWAS

    Asalin hoton, Ecowas - Cedeao/X

    Ƙungiyar bunƙasa tattalin arziƙin ƙasashen Afirka ta Yamma, ECOWAS ta bayyana goyon bayanta ga Najeriya da sauran ƙasashen ƙungiyar kan zargin ɗaukar nauyin ta'addanci da Jamhuriyar Nijar ta yi.

    Shugaban mulkin sojin Nijar, Abdourahamane Tchiani dai ya zargi Najeriya da haɗa baki da Faransa domin tayar da 'rikici' a ƙasarsa.

    ...

    A sanarwar da ECOWAS ta fitar, ta ce zarge-zargen na Nijar babu ƙamshin gaskiya a ciki.

    "Najeriya ta daɗe tana taimakon ƙasashen Afirka wajen wanzar da zaman lafiya, ba ma a yankin Afirka ta yamma kaɗai ba. Irin nasarorin da dakarun haɗin gwiwa na MNJTF, wadda Najeriya ke kan gaba wajen ɗaukar nauyi ke samu, na ƙara nuna jajircewar ƙasar a nahiyar.

    "Wannan ya sa ECOWAS ta ƙaryata zargin cewa wannan ƙasa mai ƙoƙarin jiɓintar lamarin wasu ce za ta ɗauki nauyin ta'addanci," kamar yadda sanarwar ta nuna.

    A ƙarshe ECOWAS ta yi kira ga ƙasashen yankin da su haɗa kai domin wanzar da zaman lafiya a yankin tare da nesantar jifar juna da zarge-zarge.

  19. Kuɗin da aka ware mana ba za su isa biyan albashi ba - Ƙananan hukumomi

    NULGE

    Asalin hoton, Twitter/Oyo

    Tun bayan da kotun ƙolin Najeriya ta yanke hukunci game da ba ƙananan hukumomi kuɗaɗensu kai-tsaye daga asussun gwamnatin tarayya, ake ta sa ran ganin alfanun da hakan zai haifar, musamman ga mutanen karkara da suka fi zama kusa da ƙananan hukumomin.

    Sai dai ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomin ta ƙasa, ALGON, ta bayyana wa BBC cewa kuɗaɗen da za a ware masu ba za su isa ko da biyan albashi mafi ƙaranci ba.

    A kasafin kuɗin wannan shekarar dai an ware wa ƙananan hukumomin kimanin Naira triliyan biyu.

  20. Sai mun fatattaki ƴan Houthi za mu tsagaita wuta a Yemen - Netanyahu

    Netanyahu

    Asalin hoton, EPA

    Isra'ila ta yi gargaɗin cewa yanzu ta fara ɗaukar mataki kan ƴan Houthi a Yemen, waɗanda ke kai hare-hare kan Isra'ila da kuma jiragen ruwan dakon kaya a tekun Bahar Maliya.

    Gargaɗin ya fito ne daga Firaminista Benjamin Netanyahu, bayan da Isra'ila ta ƙaddamar da wasu hare-hare ta sama kan wasu wurare a ƙasar Yemen, wanda rahotanni suka sun kashe aƙalla mutum shida.

    Netanyahu ya ce, "mun ƙuduri aniyar kawar da wannan ɓangaren ta'addancin na ƙasar Iran. Za mu dage har sai mun cimma nasarar kammala aikin."

    A nasa ɓangaren, da yake bayyana yadda ya sha tsallake rijiya da baya, Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce tazarar mitoci kaɗan ne tsakaninsa da harin da aka kai a babban filin jirgin saman Sanaa, babban birnin ƙasar.