Brazil ta lallasa Koriya ta Kudu inda za ta buga wasanta na gaba da Croatia
Brazil ta nuna dalilin da ya sa ta zama ta fi kowace kungiya a duniya bayan da ta lallasa Koriya ta Kudu a farkon rabin lokaci, inda ta ci hudu a cikin mintuna 36 na farko.
Wallafawa ranar:
Ko da yake Koriya ta Kudu farke kwallo daya a zagaye na biyu, daga Paik Seung-ho.
Yanzu haka dai, Brazil za ta fafata da Croatia a ranar Juma'a a wasan kusa da na karshe.
An nuno yadda 'yan wasan Brazil ke rike da tuta da ke ambaton Pele, fitaccen dan wasan Brazil wanda a halin yanzu ke kwance a asibiti.
Pele ya kafa kasance dan wasan da ya fi kowa zura kwallo a raga a Brazil, inda Neymar, ya ci kwallaye 76, kwallo daya kacal a bayansa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu