Yaya da Kolo Toure zasu kauracewa Manchester City
Kasar Cote d’iVoire ta yi watsi da bukatar Manchester city game da tsaikun gayyatar ‘yan uwan juna Yaya Toure da kolo Toure domin dawowa gida buga gasar cin kofin Afrika da za’a gudanar a cikin watan nan.
Wallafawa ranar:
Yanzu haka kuma ‘Yan wasan biyu ba dasu Manchester city zata buga wasan FA ba, da zata fafata tskaninta da Manchester United a ranar lahadi. Bayan kocin Cote d’Ivoire ya bukaci ‘yan wasan.
A ranar Assabar ne ‘yan wasan guda biyu zasu hadu a birnin Paris na Faransa daga nan kuma su tashi zuwa Abu Dhabi inda zasu kwashe tsawon makwanni biyu suna horo kafin mikawa zuwa Gabon da Equatorial Guinea.
Kocin Cote d’Ivoire Francois Zahoui ya fitar da jerin ‘yan wasa 25 da zasu haska a gasar, da suka hada da Didier Zokora da ke taka kwallo a kungiyar Trabzonspor ta kasar Turkiya da Emmanuel Eboue na Galatasaray, hadi da Salomon Kalou Chelsea da Didier Drogba da Gervinho Arsenal a Ingila.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu