Isa ga babban shafi

Yan bindiga sun yi wa tawagar jami’an tsaron Okowa kwanton bauna,tare da kashe ‘yan sanda uku

Jami’an ‘yan sanda uku ne suk mutu a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka yi wa tawagar jami’an tsaro na gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta kwanton bauna.Lamarin ya faru ne da misalin karfe 1:30 na rana.Ifeanyi Okowa kuma shine mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP Atiku Abubacar. 

Atiku Abubakar tare da abokin taya shi takara a zaben 2023 Ifeanyi Okowa
Atiku Abubakar tare da abokin taya shi takara a zaben 2023 Ifeanyi Okowa © TheInfoNG
Talla

Rahotanni na nuni cewa ‘yan bindigar sun kai wa tawagar jami’an tsaro hari  a unguwar Ihiala, da ke karamar hukumar Ihiala a jihar Anambra, a kudu maso gabashin Najeriya.

An ce ‘yan bindigar sun sako daya daga cikin jami’an da ba sa cikin kakin, majiyoyi sun ce jami’an na kan hanyar zuwa jihar Abia ne, inda aka ce an bukaci Okowa ya je, domin ganawa da wasu ‘ya’yan jam’iyyar PDP a jihar gabanin zaben shugaban kasa da za a yi a ranar 25 ga watan Fabrairu.

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Anambra, Tochukwu Ikenga a safiyar yau asabar, ya tabbatar da  faruwar lamarin.

Tochukwu Ikenga, mataimakin Sufeton ‘yan sanda, ya ce wadanda harin ya rutsa da su jami’an sa ne da ke aiki a sashin kula da bama-bamai na rundunar ‘yan sandan jihar Delta kuma suna kan aikin gwamnatin jihar ne.

“An kai wa jami’an hari ne kuma wasu ‘yan bindiga da ba a tantance ba sun kona motarsu,” inji shi.

A halin yanzu ana ci gaba da kokarin zakulo 'yan bindigar da suka aikata wannan aika aika," in ji Tochukwu Ikenga.

Harin dai na zuwa ne sa’o’i 24 bayan Abiye Sekibo, babban daraktan yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP a jihar Ribas, ya tsallake rijiya da baya a wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai a Fatakwal, babban birnin jihar.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.