Isa ga babban shafi

Zamu taimaka wajen kayar da PDP a zabe mai zuwa - Nyesom Wike

Gwamnan Jihar Rivers dake Najeriya, Nyesom Wike yayi barazanar taimakawa Jam’iyyar su ta PDP wajen ganin ta sha kaye a zaben shugaban kasar shekara mai zuwa, wanda Atiku Abubakar ke mata takara.

Gwamnan Jihar Rivesr kenan Nyesom Wike
Gwamnan Jihar Rivesr kenan Nyesom Wike Yasuyoshi CHIBA / AFP
Talla

Wike wanda ke takun saka da wasu jiga-jigan Jam’iyyar tun bayan shan kayen da yayi a zaben fidda gwani, ya bayyana haka ne bayan wasu daga cikin yan Jam’iyyar sun yi watsi da bukatar sa ta sauke shugaban Jam’iyyar Iyorchia Ayu daga kujerar sa, domin mayar da kujerar kudancin Najeriya.

Gwamnan ya bayyana shugaban Jam’iyyar Ayu a matsayin dan babakere wanda ke sanya bukatar kansa fiye da ta kowa, abinda yace zai sanya PDP faduwa a zabe mai zuwa.

Wike yace tunda bukatar Ayu itace faduwa a zaben shekara mai zuwa, zasu taimakawa Jam’iyyar wajen ganin ta fadi warwas kamar yadda yake bukata.

Dangane da yarfen da shugaban Jam’iyyar ya masa cewar bai san lokacin da suka kafa PDP ba, kuma shi yaro ne karami lokacin da akayi gwagwarmayar samar da Jam’iyyar, Wike ya bayyana kalaman a matsayin abinda ke nuna rashin godiya da kuma kokarin rarraba kan mambobin PDP.

Gwamnan ya bayyana cewar wadanda shugaban Jam’iyyar ke kira yara, su suka dauko shi daga kwararo, suka kuma mayar da shi shugabansu da zummar ganin ya samar mata da maslaha, amma kuwa sai rarraba kawunan jama’a yake yi.

Jam’iyyar PDP da dan takaran shugaban ta sun kwashe makwanni suna kokarin shawo kan Wike domin ganin sun kwantar da hankalin sa dan yiwa Jam’iyyar aiki, amma kuma shi ya hakikance cewar, dole shugabancin PDP ya koma kudu saboda dan takaran shugaban kasa ya fito daga arewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.