Isa ga babban shafi
Syria

Fararen hula sama da 200,000 sun tsere daga Aleppo

Hukumar Kula da 'Yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, ta ce akalla mutane 200,000 suka gudu daga garin Aleppo, dake kasar Syria, dan tsira da rayukansu, daga fafatawar da ake cigaba da yi tsaknin dakarun gwamnati da 'Yan Tawayen kasar.Jami’ar hukumar, Valerie Amos ce ta sanar da haka, yayin da take cewa, wasu daruruwan mutane sun makale, sun kuma rasa yadda za su yi a cikin garin. 

Wasu 'Yan kasar Syria na tserewa daga gidajensu
Wasu 'Yan kasar Syria na tserewa daga gidajensu Reuters/Umit Bektas
Talla

Garin Aleppo na da yawan mutane kusan miliyan 2.5 kuma shine gari na biyu mafi girma a kasar ta Syria

Amos ta bayyana damuwarta kan yadda ake anfani da muggan makamai a cikin garin.

“Ba za a iya kiyasce mutane nawa ke makale a garin na Aleppo ba a inda rikicin ya ke cigaba da karuwa”, Amos ta gayawa Kamfanin Dillancin labaran AFP.
 

Ta kara da cewa, ta damu kwarai da irin yadda ake cilla rokoki da yadda ake amfani da tankunan yaki da kuma muggan makamai a inda fararen hula ke zaune da sauran yankuna.

Mafi yawan mutane da ke ficewa a garin na Aleppo sun gudu ne zuwa kasashen Jordan, Iraq da kuma Turkey da ke kusa da kasar ta Syria ‘yan kwanakin nan.

A cewar ta wasu da yawa kuma suna makale a makarantu da sauran ma’aikatu kana suna cikin matsin rayuwa saboda matsalar ruwan sha da abinci da bargunnan kwanciya.

Duk da irin rikicin da ake fama da shi hukumar ba da agaji ta Red Cross da Majalisar Dinkin Duniya kamar yadda Kamfanin Dillancin labaran AFP ya rawaito sun ce su na kokarin kai kayan agaji.

Akalla sama da mutane 20,000 aka kashe a cikin rikicin na Syria da aka kwashe sama da watanni 16 ake yi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.