Isa ga babban shafi

Shugaban Iran zai yi aiki da manyan ƙasashe don warware rikicin nukiliya

Shugaban Iran Mas’oud Pezeshkian ya ce a shirye ƙasarsa ta ke a kawo ƙarshen zaman doya da manjan da ke tsakaninta da ƙasashen yammacin duniya, amma bisa sharaɗin sassautawa, ko ma janye takunkuman tattalin arziƙin da manyan ƙasashen suka ƙaƙaba mata.

Shugaban Iran Ma'ud Pezeshkian a zauren babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya/.
Shugaban Iran Ma'ud Pezeshkian a zauren babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya/. AP - Pamela Smith
Talla

Sabon tayin na Iran da ta gabatar a babban taron zauren Majalisar Ɗinkin Duniya da ke gudana a birnin New York, na zuwa ne bayan gazawar dukkanin yunƙurin da aka yi na farfaɗo da yarjejeniyar nukiliyar da aka ƙulla tsakaninta da manyan ƙasashen Turai ciki har da Amurka a shekarar 2015.

Yarjejeniyar nukiliyar da tsohon shugaban Amurkan Donald Trump ya fice daga cikinta a shekarar 2018 dai ta ƙayyade wa Iran damar tace makamashin Uranium ne zuwa matakin kashi 3.67, sharaɗin da manyan ƙasashen na yamma ke zargin Iran ɗin da ketarewa.

Amurka, da ƙawayenta na Turai da kuma Isra’ila na zargin Iran da yin amfani da shirinta na Nukiliya wajen ƙoƙarin ƙera makaman ƙare dangi, sai dai har yanzu ƙasar na cigaba da musanta wannan tuhuma, tare da nanata cewar shirin Nukiliyar tata na zaman lafiya ne zalla.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.