Isa ga babban shafi
Taron Majalisar Ɗinkin Duniya

MDD na ƙoƙarin ɗinke ɓarakar da ke tsakanin ƙasashen duniya

Babban magatakardan Majalisar Ɗinkin Duniya, António Guterres, ya ƙaddamar da wani taron yanayi mai taken, ‘Taro Don Makomarmu’ a matsayin wani ɓangare na taron babban zauren majalisar, inda wasu jagorori su ka yi gargaɗi kan yadda ake ci gaba da samun rashin yarda a tsakanin ƙasashe, a yayin da bala’o’i masu nasaba da ke ci gaba da ta’azzara.

Babban Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres
Babban Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres © David Dee Delgado / Reuters
Talla

Jagororin ƙasashe sun yi jawabi ga taron, bayan da suka amince da wata yarjejeniya a game da makomar duniya, wadda aka cimma da zummar tabbatarwa tare da yauƙaƙa haɗin kai tsakanin ƙasashe, inda da dama ke kira da a gaggauta ba su damar amfana da kuɗaɗen da aka tanada don tinkarar sauyin yanayi.

Guterres ya shaida wa jagororin cewa, kalubalen sun ɗauki hanyar fin ƙarfin mahukunta, musamman ma yadda ci gaban fasahar zamani  ke taimakawa wajen yaɗa bayanai marasa tushe a kan yanayi, lamarin da ke ta’azzara rashin yarda da rarrabuwar kawuna.

Firaministar Barbados, Mia Mottley ta jaddada kashedin Guterres a kan batun sake lale a game da yadda  ake tafiyar da hukumomin duniya, ta inda za su iya tinkarar matsaloli tare da taimaka wa waɗanda su ka fi kasancewa cikin matukar buƙata.

Ƙungiyar  yanayin, wanda ke tsara shirin makon yanayi ya zayyano taruka dabam-dabam har 900 masu nasaba da yanayi waɗanda za su gudana a wannan makon, waɗanda kamfanonin kasa-da-ƙasa da ƙungiyoyi masu zaman kansu da gwamnatoci za su ɗauki nauyin shiryawa.

A waje ɗaya kuma a cikin wannan makon, shugaban Amurka, Joe Biden zai gabatar da jawabi a wani taro da ya samu halartar jaruma, kuma mai fafutukar kare muhalli, Jane Fonda da shugaban bankin duniya, Ajay Banga da sauransu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.