Isa ga babban shafi

FBI na ci gaba da bincike kan harin da aka sake kai wa Trump

Hukumar Tsaro ta farin kaya ta Amurka FBI, ta ce tsohon shugaban kasar kuma ɗan takarar shugabancin ƙasa a jam'iyyar Republican Donald Trump, na cikin ƙoshin lafiya bayan da ta ce anyi yunkurin kashe shi a wani hari da aka kai masa a filin wasan ƙwallon gora na Trump golf course da ke jihar Florida a jiya Lahadi.

Tsohon shugaban Amurka Donald Trump.
Tsohon shugaban Amurka Donald Trump. AP - Alex Brandon
Talla

A cewar Hukumar ta FBI, bayan harba bingidar da maharin ya yi, ya yar da ita ya kuma hau mota da nufin ya tsere wa daga wajen, sai dai da taimakon wani wanda ya shaida faruwar lamarin, sun samu nasarar kama wanda ake zargin kuma ana nan ana ci gaba da gudanar da bincike kan sa.

Wannan dai shi ne hari na baya-baya da aka kaiwa tsohon shugaban ƙasar ta Amurka Donald Trump, domin watanni biyu da suka gabata anyi yunkurin hallakashi a lokacin yaƙin neman zabe a Pennsylvania, inda alburushi ya goge shi a kunne.

Tun daga wancan lokacin ne kuma tsohon shugaban ƙasar na Amurka ya ƙara tsaurara matakan tsaron da ke bashi kariya.

Tuni dai fadar White House ta ce shugaban ƙasar Joe Biden da kuma mataimakiyarsa kuma ƴar takarar jami’iyar Democratic Kamala Harris, suka jajanta masa bisa faruwar iftila’in.

A wata sanarwa da Harris ta fitar ta ce abin farin ciki ne yadda Allah ya kare Trump daga wannan hari, sannan ta ce tashin hankali ba zai samu matsugunni a Amurka ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.