Isa ga babban shafi

An tafka zazzafar muhawara karon farko tsakanin Trump da Harris

A safiyar yau ne aka tafka zazzafar muhawara karon farko tsakanin ƴan takarar shugabancin Amurka Kamala Harris ta jam’iyar Democrat da kuma Donald Trump na jam’iyar Republican.Khamis Saleh ya bibiyi yadda muhawar ta gudana, ga kuma rahoton da ya hada mana.

Wannan ce muhawara karon farko tsakanin ƴan takarar na Amurka gabanin zaɓen da ke tafe a cikin watan Nuwamba.
Wannan ce muhawara karon farko tsakanin ƴan takarar na Amurka gabanin zaɓen da ke tafe a cikin watan Nuwamba. AP
Talla

Trump ya yi kakkausar suka ga salon da Democrat ta yi amfani da shi wajen tunƙarar rikicin gabas ta tsakiya ya na mai cewa idan har da shi ne akan mulki ko shakka babu yaƙin da faruwa a Gaza ba zai taɓa faruwa ba.

A ɓangare guda Harris ta bayyana shirinta na samar da ƙasashe biyu da nufin warware rikicin tsawon shekaru tsakanin Isra'ila da Falasɗinu.

Dona
Donald Trump da Kamala Harris yayin muhawara. AFP - SAUL LOEB

Dukkaninsu sun caccaki juna game da yadda Amurka ta tunƙari yaƙi da Taliban, inda Harris ta ce Trump ya tafka abin kunya bayan zaman tattaunawa da wakilcin mayaƙan na Taliban daga Afghanistan yayinda shi kuma soki gwamnatin Democrat kan yadda ta gaza cika alƙawarin kwashe Amurkawan da ke Ƙabul bayan Taliban ta ƙwace mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.