Isa ga babban shafi

An nada sabon firaministan rikon kwarya a Pakistan

Firaministan Pakistan da jagoran 'Yan adawar kasar sun nada Anwar-rul-Haq Kakar, a matsayin fira ministan rikon kwarya, don shirya harkokin zaben da aka sanya gaba a kasar da ke fama da kalubalen siyasa da kuma tattalin arziki. 

Fara ministan Pakistan Shehbaz Sharif.
Fara ministan Pakistan Shehbaz Sharif. AP - Salvatore Di Nolfi
Talla

Sanata kuma Dan siyasar Pakistan da ke lardin Balochistan a shiyar kudu maso yammacin kasar, zai na da ministocin sa da za su gudanar da ayyukan gwamnati har zuwa lokacin da za a zabi wanda zai dare kujerar.

A cewar  ofishin Firaministan Pakistan Shehbaz Sharif ta re da jagoran ‘yan adawar kasar Raja Riaz ne suka amince da wannan nadin, don jagorantar  harkokin zaben da zai gudana.

Tuni firaministan na Pakistan da jagoran ‘Yan adawar suka rattaba hannu kan wannan muhimmin shirin da za a mika ga ofishin shugaban kasar don neman sahalewar sa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.