Isa ga babban shafi

Ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya na fuskantar gibin kudade

Ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya na fuskantar gibin kudade a bana, inda kashi uku  na dalar Amurka biliyan 48.7 da ake bukata ya zuwa yanzu yayin da bukatun duniya suka zarce alkawuran da aka dauka, in ji Jens Laerke, kakakin ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya (OCHA).

Hukumomin bayar da agaji a kasar Congo sun kadamar da wani shirin jinkai  2015 wajen samar da ruwan sha mai tsafta  ga kimanin mutane milin 5,2.
Hukumomin bayar da agaji a kasar Congo sun kadamar da wani shirin jinkai 2015 wajen samar da ruwan sha mai tsafta ga kimanin mutane milin 5,2. Photo OCHA/ Philippe Kropf
Talla

Ana buƙatar kuɗin don taimakawa kusan mutane miliyan 204 a duk faɗin Duniya yayin rikice-rikice na makamai da bala'o'i, irin su yaƙin Ukraine da fari a Afirka ta Kudu, sun bayyana a matsayin manyan abubuwan da ke haifar da "rikicin wanda ke yin barazana ga rayuwar gaba ɗayan al'ummai.

Kasashe masu tasowa na fama da tsadar abinci,banda haka ga karancin taimako daga manyan kasashen Duniya,sai al'amarin rashin tsaro da ya tilasatawa da dama daga cikin mazauna yankunan karkara ficewa daga yankunan su a wasu kasashen Sahel.

A karshe,karin haraji ya kawo cikas ga harakokin kasuwanci na kananan yan kasuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.