Venezuela
Hugo Chavez ya koma jinya a kasar Cuba
Yau ake saran shugaban kasar Venezuela, Hugo Chavez, zai tafi kasar Cuba dan yi masa aiki kan cutar sankarar da yake fama da ita, wanda hakan shine karo na hudu da Chavez zai tafi jinya.A jawabin da ya yiwa yan kasar, shugaba Chavez ya mika ragamar tafi da kasar ga mataimakin sa, Maduro, inda yake cewa koda lafiyar sa ta tabarbare, yana bukatar ‘Yan kasar su zabi Maduro a matsayin shugaban kasa.
Wallafawa ranar: