Isa ga babban shafi

Majalisar Kenya ta fara yunƙurin tsige mataimakin shugaban ƙasa

Ƴan majalisar dokokin Kenya sun fara shirin tsige mataimakin shugaban ƙasar Rigathi Gachagua saboda zargin da suke masa na sabawa kundin tsarin mulkin kasa, sakamakon tsamin dangantakar da ke tsakanin sa da shugaban ƙasa William Ruto.

Rigathi Gachagua mataimakin shugaban ƙasar Kenya yayin rantsuwar kama aiki.
Rigathi Gachagua mataimakin shugaban ƙasar Kenya yayin rantsuwar kama aiki. © SIMON MAINA / AFP
Talla

Wasu ƴan majalisun dokokin Kenyan ne suka gabatar da ƙudirin tsige mataimakin shugaban ƙasar, inda tuni suka fara zama kan kudurin a ranar Talata, al’amari da ke kara fito da rashin jituwa tsakanin ƴanƴan jam’iyyar mai mulki.

Tun a watan Maris ne siyasar ƙasar da ke gabashin Afirka ta fada cikin rudani, sakamakon kazamin zanga-zanga kan tsadar rayuwa da ƙarin haraji da matasan ƙasar suka gudanar.

Ana zargin Gachagua da yi wa gwamnati zagon ƙasa, da cikin cin hanci da rashawa da rashin biyayya da gudanar da siyasar kabilanci da wasu laifuffuka.

Ƴan majalisar wakilai 291 ne suka rattaba hannu kan amincewa da ƙudirin, wanda ya zarce mafi karancin da aka bukata na wakilai 117.

Kakakin majalisar dokokin ƙasar, Moses Wetangula, ya ce kudirin, wanda ɗan majalisa Mutuse Eckomas Mwengi, daga jam'iyyar mai mulki ya gabatar -- ya cika dukkan sharuddan tsarin mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.