Isa ga babban shafi

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch ta bukaci a gudabar da bincike a Burkina Faso

A Burkina Faso,kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch (HRW) ta yi kira a jiya Juma'a da a gudanar da "bincike ba tare da nuna son kai ba" biyo bayan wasu  faya-fan bidiyo da ke nuna ta yada wasu dakarun kasar ke fede gawarwakin wasu mayaka da kuma cin naman su.

Shugaban Majalisar sojin Burkina Faso Kyaftin Ibrahim Traore
Shugaban Majalisar sojin Burkina Faso Kyaftin Ibrahim Traore AFP - OLYMPIA DE MAISMONT
Talla

An watsa faifan bidiyo a shafukan sada zumunta a karshen watan Yuli, wanda yake nuna wasu mutane sanye da kayan sojoji da za a iya gane su, biyu daga cikinsu suna amfani da wukake wajen yanke naman jikin wasu mayaka da suka kasha.

Shugaban Majalisar sojin Burkina Faso,Kyaftin Ibrahim Traore
Shugaban Majalisar sojin Burkina Faso,Kyaftin Ibrahim Traore AFP - OLYMPIA DE MAISMONT

Ana dai ganin wani mutum sanye da kakin soji dauke da tutar Burkina Faso da ake gani a kafadarsa ta hagu yana jingina da gawar da aka yanke a kasa" kafin ya "yanke naman" daga gawar, kamar dai yada kungiyar ta tabbatar.

Wadan runduna ta Burkina Faso na bayyana cewa a cikin yaren Faransaci suna karkashin Bataliya ta 15 (BIR-15), wata runduna ta musamman da ke da hannu a hare-hare  a kan kungiyoyin yan ta’adda masu dauke da makamai.

Dakarun Burkina Faso
Dakarun Burkina Faso © ISSOUF SANOGO / AFP

A karshe wannan kungiya ta bukaci hukumomin na Burkina Faso su gaggauta kama mutanen da aka samu da hannu wajen aikata wannan ta’asa da kuma  gurfanar da su gaban kuliya, ba tare da la'akari da matsayinsu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.