Isa ga babban shafi

Majalisar Togo ta amince da kundin tsarin mulkin kasar da ta yiwa kwaskwarima

‘Yan majalisar Togo sun amine da kwaskwarimar da aka yi wa kundin tsarin mulkin kasar, wanda ya sauya tsarin mulkin kasar daga na shugaban kasa mai cikakken iko zuwa na Faraminista.

Shugaban kasar Togo Faure Gnassingbé.
Shugaban kasar Togo Faure Gnassingbé. © Gnassingbe Twitter
Talla

Sabon daftarin dokar dai ya nuna cewa, ‘yan majalisa ne za su rinka zabar shugaban kasa na tsawon wa’adi guda, ba jama’ar kasar ba, kamar yadda aka saba a baya.

Wannan sauyin dai na zuwa ne kasa da wata guda da za a gudanar da zaben ‘yan majalisar dokoki a kasar ta Togo, toh sai dai ba a san lokacin da za a fara amfani da sabon kundin tsarin mulkin ba da ‘yan majalisu 89 suka amince da shi, daya kuma ya hau kujerar naki sannan ragowar dayan ya kauracewa kada kuri’ar amincewa.

‘Yan majalisar da suka fito daga jam’iyar da ke mulkin kasar ta UNIR ne suka gabatar da kudirin sauya fasalin kundin tsarin mulkin kasar da kuma amincewa da shi.

Jam’iyar adawar kasar da ta kauracewa shiga zaben ‘yan majalisar kasar da aka gudanar a shekarar 2018 saboda dalilan sabawa ka’ida, ba tada wakilci a majalisar kasar.

Kundin tsari mulkin da kasar ke amfani da shi yanzu haka an kirkire shi ne tun 1992, to amma an yi masa gyare-gyare sau da dama, kuma na karshe shi ne wanda aka yi a 1999, a karkashinsa, ana zaben shugaban kasa wa’adin shekaru 5 ne tare da damar sake tsayawa karo na biyu kawai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.