Isra'ila ta ci gaba da ruwan bama-bamai a Gaza
A rana ta biyu bayan karewar yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas, Isra’ila ta ci gaba da ruwan bama-bamai a yankin Gaza, bayan da aka gaza cimma wata yarjejeniyar duk kuwa da bukatar hakan da kasashen duniya suka gabatar.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Kakakin rundunar tsaron Isra'ila Jonathan Conricus ya shaidawa manema labarai a yau Asabar cewar suna kaiwa Hamas hari ne.
"Abin da muke yi yanzu shi ne kai farmaki kan mayakan Hamas a duk fadin zirin Gaza."
Ma’aikatar kula da lafiyar yankin Falasdinu, ta ce tun bayan kaddamar da sabbin hare-hare da Isra’ila ta yi a yankin Gaza a jiya Juma’a, kimanin mutane dari 2 ne suka rasa rayukansu.
Bangarorin biyu dai na zargin juna da gazawa wajen tsawaita yarjejeniyar tsawaita wuta, inda Isra’ila ta yi ikirarin cewar Hamas ta yi yunkurin kai mata hari rokoki a lokacin da aka tsagaita wuta da kuma gazawarta wajen fidda sunayen sauran mutanen da take rike dasu.
Fara ministan Belgium Alexandre De Croo ya shaidawa manema labarai a wajen Yanayi na duniya COP28 da ke gudana a Dubai cewar, sun tattauna da takwaransa na Isra’ila Benjamin Netanyahu, kan kawo karshen kashe fararen hula a yakin.
Ya kuma ce suna fatan ci gaba da amfani da iyakar Rafah, wacce ta kasance a rufe tun bayan sake kaddamar da hare-haren da Isra'ila ta yi, don kai kayan agaji yankin na Gaza.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu