Isa ga babban shafi
Mali

MDD za ta tsawaita aikin dakarunta a Mali

Majalisar Dinkin Duniya na shirin tsawaita aikin dakarunta na wanzar da zaman lafiya a kasar Mali, a yayin da jami’an da ke aikin tare da dakarun ke korafin rashin samun wadatar tallafin kudi da rashin samun hadin kan al’umma domin kawo karshen hasarar rayuka.

Dakarun MINUSMA da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Mali
Dakarun MINUSMA da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Mali REUTERS/Adama Diarra
Talla

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban ki-Moon ya bukaci kwamitin tsaro na Majalisar ya amince da bukatar kara tura wasu Dakaru 2,500 da suka hada da ‘yan sandan kasar, domin tsawaita ayyukansu har zuwa Yunin 2017.

Har yanzu dai ana ci gaba da samun hare haren mayakan da ke da’war Jihadi a Mali, inda dakarun wanzar da zaman lafiya 68 aka kashe tun kaddamar da aikinsu a watan Afrilun 2013.

Mayakan Ansar Dine da al-Qaeda, sun tsawwala hare-harensu a kasar, tare da yawaita kai harin kwantan-bauna a sansanonin soji a arewacin Mali.

Aikin dakarun Majalisar Dinkin Duniya da ake kira MINUSMA ya shafi sa ido ga kokarin tabbatar da yarjejeniyar sulhu da gwamnati ta sanya wa hannu a 2015 tare da sojojin sa-kai da bangaren kungiyoyin tawaye da ke yakin tabbatar da kasar AZAWAD a arewacin Mali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.