Shirin lafiya Jari ya yi nazari kan matsalar cutar kansar bakin mahaifa da kuma kokarin gwamnatin Nijar na taimaka wa masu fama da cutar da magani kyauta.
Sauran kashi-kashi
-
Tsanantar cutar ƙoda da abubuwan da ke haddasa ta a tsakanin al'umma
A wannan makon shirin ya mayar da hankali ne kan abubuwan da ke haddasa cutar koda, la'akari da yadda cutar ke tsananta a wannan lokaci musamman a kasashe irin Najeriya, sabanin a lokutan baya da ba kasafai ake ganinta ba, baya ga karancin wuraren wankin kodar da ake fama dasu wato dialysis centers a turance.23/09/202409:44 -
Abubuwan da ke haddasa tsinkewar laka ga ɗan Adam
Shirin lafiya jarice na wannan mako ya mayar da hankali ne kan cutar katsewar laka wacce ke iya afkuwa a sanadiyar hadarin mota ko makamantansu da rikice-rikice ko fadowa daga wurare masu tudu da dai sauransu.20/09/202409:21 -
Yawaitar masu fama da lallurar laka a sassan Najeriya
A wannan mako shirin zai mayar da hankali game da cuta ko kuma ‘‘lalurar katsewar Laka’’ wato Spinal cord Injury, lalurar da a baya-bayan nan alƙaluma ke nuna yawaitar masu fama da ita a sassan Najeriya, walau sakamakon haɗarin mota ko rikici dama sauran dalilai.16/09/202409:58 -
Ƙaruwar ƙananan yara da ke fama da matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki
A wannan makon shirin zai mayar da hankali kan ƙaruwar ƙananan yaran da ke fama da cutar yunwa ko kuma Tamowa a yankunan da ke fama da ƙarancin abinci, cikinsu kuwa har da Nijar, ƙasar da alƙaluman 2021 ke cewa akwai ƙananan yara ƴan ƙasa da shekaru 5 akalla miliyan 1 da dubu 800 da ke fama da rashin abinci mai gina jiki.02/09/202410:16 -
Hatsarin da ke cikin amfani da maganin ƙwari wajen adana kayan abinci
Shirin 'Lafiya Jari Ce' na wannan makon zai mayar da hankalli ne a kan gargaɗin da hukumar kiyaye ingancin abinci da magunguna a Najeriya, wato NAFDAC ta yi a kan hatsarin da ke tattare da amfani da maganin kashe ƙwari na Sniper a wajen adana kayan abinci domin kare su daga ƙwari. NAFDACdai ta jaddada haramcin da ta yi a kan amfani da wannan magani da ma sshigowa da shi Najeriya, bayan da ce bincikenta ya tabbatar da cewa maganin yana haddasa cutuka da suka haɗa da cancer.22/07/202409:50