An cimma yarjejeniyar mayar da kabilar Rohingya gida
Kasashen Myanmar da Bangladesh sun sanya hannu kan yarjejeniyar mayar da ‘yan kabilar Rohingya gida, wadanda suka tsere a sanadiyyar rikicin yankin Rakhine.
Wallafawa ranar:
Hakan na zuwa ne bayan da kasashen duniya ke cigaba da matsa lamba dangane da rikicin, wanda kasar Amurka ta bayyana a matsayin yunkurin kawar da kabilar ta Rohingya daga doron kasa.
Bayan kwashe makwanni ana ja-in-ja game da ka’idojin yarjejeniyar, kasashen biyu sun cimma matsaya, a lokacin da jagorar kasar Myanmar Aung San Suu Kyi ta gana da ministan harkokin kasashen waje na Bangladesh Mahmood Ali a babban birnin kasar na Myanmar.
A cikin wani takaitaccen bayani da ya yi wa manema labarai, Ali ya ce wannan ne matakin farko na yarjejeniyar. Sai dai ba a samu bayanai game da saurarn abubuwan da ke kunshe a cikinta ba.
Wasu daga cikin batutuwan da ba a sani ba su ne yawan ‘yangudun hijira da za a bari su koma gida da kuma tsawon lokacin da za a kwashe ana aikin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu