Korea ta Kudu zata wargaza Jami'an tsaro a Teku
Shugabar Kasar Koriya ta kudu, Park Geun-hye ta ce zata wargaza jami'an tsaron tekun kasar saboda sakacin da aka same su da yi wajen aikin ceton dalibai sama da 300 da suka mutu a wani hadarin jirgin ruwa a kasar. Shugabar ta kuma nemi gafarar al'ummar kasar, inda tace za'a kafa wata sabuwar runduna da zata dace da zamani, bayan ta dauki alhakin matsalar da aka samu a matsayinta na shugaba.
Wallafawa ranar:
A ranar 16 ga watan Afrilu ne jirgin ruwa ya kife a teku inda aka samu mutuwar mutanen Korea ta kudu kimanin 300 galibinsu Yara kanana daliban Makaranta.
Jirgin ruwa yana dauke ne da mutane 325, kuma an tabbatar da mutuwar 286, yayin da 18 suka bata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu