Jump to content

Fati Washa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Fati Washa
Rayuwa
Haihuwa 21 ga Faburairu, 1993 (31 shekaru)
ƙasa Najeriya
Sana'a
Sana'a jarumi

Fatima Abdullahi Washa Wacce aka fi sani da (fati washa) yar wasan Hausa ce a masana'antar fim ta Kanniwod.

An haifeta a ranar 21 ga watan Fabrairun, shekara ta alif dari tara da casa'in (1990),a jihar Bauchi.[1][2]

Fati washa jaruma ce a Masana'antar Hausa fim, wacce ake ji da ita tayi tashe yanzun tadanyi sanyi, ta Kuma karo wuta a sabbin fina finanta.ansa mata suna washa ne saboda yawan fara'arta da dariya.fati washa tana daga cikin jerin mata da ake sakasu a jerin manyan yammatan kanniwud, washa fati batai aure bah , matakin karatun ta sakandari satifiket ke gareta, Amma kuma tanada burin cigaba da karatun ta, washa fati ta kware wajen Hawa wakokin Hausa ,sannan Kuma tana taka muhimmiyar rawa a fannin acting , dakuma rawa ta iya rawa, washa fati tayi soyayyah da babban jarumi adamu zango, wacce har sun dau hanyar aure maganar ta lalace,tayi fina finai da dama a kanniwud.musamman yanzun data zama acikin Shirin fim Mai suna labarina. Wanda rashin tsohuwar jarumar fim din nafisa Abdullahi yasa aka Nemo ita fati washa ta maye gurbinta, wanna yazama babbar nasara da daukaka ga jarumar a shigarta cikin Shirin na labarinah.sannan takara Wani suna da fice a wnnn Shirin na manyan mata na hadiza Aliyu gabon.

Tayi fina finai a baya da dama da suka hada da:

  • Na Gaba
  • Makahon Gida
  • Make Da Bake
  • Ya daga Allah
  • ‘Yar Tasha
  • Ana Wata ga Wata
  • Baya da Kura
  • Fari Da Baki
  • Farida
  • Gaba da Gabanta
  • Hadarin Gabas
  • Hindu - Anarin Africanarya na Afirka
  • Hisabi
  • Jaraba
  • Karfen Nasara
  • Makahon Gida
  • Niqab
  • Dangin Miji
  • Badda kama
  • Mijin biza
  • Matar mijinah
  • Labarina
  • Manyan mata
  • Nafi haidar
  • Husna da huzna
  • Karfen kafa
  • Afrah
    • Da sauran su
Fayil:Fati Washa.jpg
washa saboda dariyanta aka sa mata washa
  1. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-01-06. Retrieved 2023-01-06.
  2. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-06-05. Retrieved 2020-11-04.

3 https://notjustnorth.com/fati-washa-net-worth-and-biography-updated-2023/ Archived 2023-06-23 at the Wayback Machine