Benjamin Komla Kpodo
Benjamin Komla Kpodo | |||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|
7 ga Janairu, 2021 - District: Ho Central Constituency (en) Election: 2020 Ghanaian general election (en)
7 ga Janairu, 2017 - District: Ho Central Constituency (en) Election: 2016 Ghanaian general election (en)
7 ga Janairu, 2013 - 6 ga Janairu, 2017 District: Ho Central Constituency (en) Election: 2012 Ghanaian general election (en) | |||||||
Rayuwa | |||||||
Haihuwa | 22 Disamba 1953 (70 shekaru) | ||||||
ƙasa | Ghana | ||||||
Karatu | |||||||
Makaranta |
University of Ghana Digiri a kimiyya : business administration (en) Jami'ar jahar Lagos Master of Science (en) : accounting (en) | ||||||
Harsuna | Turanci | ||||||
Sana'a | |||||||
Sana'a | ɗan siyasa da accountant (en) | ||||||
Imani | |||||||
Addini | Kiristanci | ||||||
Jam'iyar siyasa | National Democratic Congress (en) |
Benjamin Komla Kpodo (An haifeshi ranar 22 ga watan Disamba, 1953) ɗan siyasan ƙasar Ghana ne kuma ɗan majalisar dokoki ta bakwai na Jamhuriya ta huɗu ta Ghana mai wakiltar Mazabar Ho ta Tsakiya a Yankin Volta akan tikitin Jam'iyyar National Democratic Congress.[1]
Rayuwar mutum
[gyara sashe | gyara masomin]Shi Kirista ne (Evangelical Presbyterian).
Yana da aure, yana da yara bakwai.[1]
Rayuwar farko da ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Kpodo a ranar 22 ga Disamba, 1953. Ya fito ne daga Tanyigbe, wani gari a Yankin Volta na Ghana.[1] Ya sami digirinsa na farko a zabin Gudanarwa-Accounting daga Jami'ar Ghana a 1980. Ya sami digiri na biyu na kimiyyar lissafi a Jami'ar Legas a 1991.[1]
Siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]Kpodo memba ne na National Democratic Congress (NDC). A cikin 2012, ya yi takarar kujerar Ho Central akan tikitin majalisar NDC ta shida na jamhuriya ta huɗu kuma ya ci nasara.[1] Ya ci gaba da rike kujerar sa a babban zaben kasar Ghana na shekarar 2016, inda ya lashe kashi 79.5% na kuri'un.[2] A zaben 2020, ya lashe kashi 85% na kuri'un don sake rike kujerar sa.[3]
Aiki
[gyara sashe | gyara masomin]- Jami'in Kudi, Jami'ar Ilimi, Winneba[1]
- Dan majalisa (7 ga Janairu, 2013 - yanzu; wa'adi na biyu)[1]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 1.2 1.3 1.4 1.5 1.6 "Ghana MPs - MP Details - Kpodo, Komla Benjamin". www.ghanamps.com. Retrieved 2020-02-06.
- ↑ "2016 Election - Ho Central Constituency Results". Ghana Elections - Peace FM. Retrieved 12 January 2021.
- ↑ "2020 Election - Ho Central Constituency Results". Ghana Elections - Peace FM. Retrieved 12 January 2021.