Bakonmu a Yau
A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban daban domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya. wani lokacin kuma wasu manyan jami'an gwamnati da masu fada aji sukan kawo muna ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da suka shafe su ko kuma ci gaban kasa.
Ci gaban karatuSaurari kashin karshe
Daukacin kashi-kashi
-
Shugaban matasa Muntaqa Abdulhadi Dabo kan taron matasan da Tinubu zai shirya
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana shirin gudanar da wani taron matasa na kasa domin basu damar tattauna matsalolin da suka addabe su da zummar share musu hawaye.02/10/202403:33 -
Sanata Mamman Abubakar Danmusa kan samun ƴancin kan Najeriya
Yau Najeriya ke cika shekaru 64 da samun 'yancin kai daga Turawan Ingila, inda 'yan kasar ke tilawar irin ci gaban da aka samu da kuma matsalolin da aka fuskanta a kokarin ganin ci gabar kasar. Domin tattauna wannan batu, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da daya daga cikin 'yan mazan jiya, wadanda suka ga gwagwarmayar neman 'yancin, kan asuka taka rawa a bangaren jagorancinta, wato Sanata Mamman Abubakar Danmusa, tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Jamhuriya ta 2.01/10/202403:39 -
Ibrahim Garba Wala game da halin da ake ciki na bada agaji a Maiduguri
Akalla makwanni 3 bayan ambaliyar da ta yiwa mazauna birnin Maiduguri illa, har yanzu wasu daga cikin wadanda ibtila'in ta ritsa da su na cikin mawuyacin hali, ya yin da ake ci gaba da gudanar da aikin jinkai. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Ibrahim Garba Wala, daya daga cikin shugabannin kungiyoyin da ke aikin taimakawa wadanda hadarin ya ritsa da su.30/09/202403:29 -
Yusuf Tuggar a kan Najeriya da kujerar dindindin a kwamitin Tsaro MDD
Kamar yadda wata kila kuka ji a cikin labaran duniya, Ministan harkokin wajen Najeriya, Ambassada Yusuf Tuggar ya bayyana manyan dalilan da ya kamata a yi dubi da su domin sanya kasar a matsayin mambar kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya. Shugaban Sashen Hausa na RFI, Mr Joseph Penney ya tattauna da ministan a zauren Majalisar dake ci gaba da gudanar da taronta a New York ta kasar Amurka, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana.27/09/202403:30 -
Hukumar GIABA ta shirya taron fadakar da 'yan kasuwa da masu masana'antu da kuma lauyoyi
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasashen Afirka ta Yamma, wato GIABA ta shirya wani taron fadakar da 'yan kasuwa da masu masana'antu da kuma lauyoyi a kan hakkin da ya rataya a kansu na kin bada dama ga masu halarta kudaden haramun ko kuma 'yan ta'adad su yi amfani da su wajen boye kudaden sata. Taron na kwanaki 2 na gudana ne a birnin Lagos. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da mai magana da yawun GIABA Mr Timothy Melaye, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana.26/09/202403:19 -
Dokta Abdulhakim Garba Funtua kan hare-haren Isra'ila a Lebanon
Kasashen duniya sun fara mayar da martani dangane da kazamin hare haren da Isra'ila ke kai wa a yankin kudancin Lebanon wanda a jiya kawai ya kai ga hallaka mutane kusan 300. Cikin wadanda suka bayyana damuwa da yadda yakin Isra'ilar ke fadada har da Sakatare Janar na Majalisar dinkin duniya Antonio Guterres. Dangane da wannan yaki Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Abdulhakeem Garba Funtua na Babbar Kwalejin Fasaha dake Kaduna, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana.24/09/202403:35 -
Ambasada Abubakar Chika kan fara taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Yau ake fara taron babban zauren Majalisar dinkin duniya karo na 79, wanda ake saran ya gudanar da mahawara a kan batutuwa da dama cikin su harda sabon daftarin majalisar wanda ya kunshi sauyin yanayi da rikice rikice da matsalar sauyin yanayi da rashin shugabanci na gari tare da matsalar yunwa. Dangane da wannan taro Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Ambasada Abubakar Chika, tsohon jakadan Najeriya a kasar Iran, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana.23/09/202403:33 -
Dokta Kasum Ƙurfi a kan taƙaddamar kamfanin NNPCL da matatar Ɗangote
Ga alama har yanzu tsuguni bata kare ba tsakanin kamfanin Dangote da kuma na NNPC dangane da takaddamar da ta biyo bayan fara aikin matatar mansa a Lagos. Rahotanni sun ce har yanzu ana takun saka a tsakanin bangarorin biyu. Dangane da wannan dambarwa Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Kasum Garba Kurfi, masanin tattalin arziki, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana.20/09/202403:46 -
Wasu daga cikin muhimman labarai da jaridar Aminiya ta wallafa a wannan mako
Kamar dai kowane mako, a yau juma’a ma jaridar Aminiya da ake wallafa ta a Najeriya ta sake fitowa ɗauke da dimbin labarai da suka shafi fannoni daban nan na rayuwa. Kuma Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Muƙaddashin Editan jaridar Muhammad Amin Ahmed domin jin karin bayani dangane da labaran da suke ɗauke da su a wannan karo. domin sauraron cikakken shirin, a latsa alamar sauti.20/09/202403:36 -
Babu wanda muka kora daga sansanin ƴan gudun hijira - Babagana Umara Zulum
A karon farko bayan gagarumar ambaliyar da ta shafi birnin Maiduguri, Gwamnan Jihar Babagana Umaara Zulum ya bayyana girmar matsalar da kuma kokarin da suke wajen tinkarar ta a hira ta musamman da RFI Hausa.19/09/202403:47 -
Gwamnatin jihar Borno ta bukaci al'umar birnin Maiduguri dasu kiyaye abinda zasu ci ko su sha
Gwamnatin Jihar Barno da ke Najeriya ta gargadi mazauna birnin Maiduguri da su kaucewa cin kayan abinci da ruwan shan da aka dauko daga yankunan da aka samu ambaliya, domin samun kariya. Hukumomin sun ce wadannan kayayyaki na dauke da sinadarin dake fita daga gawarwaki da masai da wasu na dabam da ka iya haifar da cututtuka. Dangane da wannan gargadi Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Balarabe Sani Garko na Jmai'ar Ahmadu Bello dake Zaria,kuma ga yadda zantawarsu ta gudana.18/09/202403:17 -
Dr Aliyu Dala kan ambaliyar da ta mamaye akasarin birnin Maiduguri
Wani masani ɗan jihar Bornon Najeriya Dr Aliyu Dala ya danganta ambaliyar da ta mamaye akasarin birnin Maiduguri da sakacin jami'an gwamnati. Dr Dala wanda ke cikin ƙungiyar ƙwararrun ƴan Arewacin Najeriya mazauna Turai ya ce sun yi nazari akan matsalar ambaliyar kuma sun gabatar da rahoto a kan matakan da ya dace a dauka, cikin su harda na Maiduguri amma babu abinda aka yi a kai.17/09/202403:31 -
Sheikh Mansur Ibrahim a kan Maulidi
Al’ummar musulmi a sassan duniya na gudanar da bukukuwan Mauludi, domin tunawa da ranar da aka haifi annabi Muhammad mai tsira da amincin Allah.To domin sanin muhimmancin wannan rana ga musulmi, Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Sheikh Mansur Ibrahim da ke garin Kaduna a Najeriya.16/09/202403:30 -
Attahiru Bafarawa: Rashin haɗin kai tsakanin dattawan arewa
A Najeriya, ga alamu ba dukannin mutanen Arewacin ƙasar ne suka yarda da irin rawar ƙungiyar Dattawan yankin wato Arewa Consultative Forum ke takawa don haɗa kan jama’a da kuma kare muradun alummar yankin ba.12/09/202403:12 -
Tattaunawa da Dr Moussa Hassan Ousseini kan taron sauyin yanayi a Nijar
Kwararru game da matsalar sauyin yanayi da kuma wakilan gwamnatoci da na ƙungiyoyi, sun fara gudanar da wani taron kwanaki uku a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar, domin tattauna matsalar sauyin yanayi a Yankin Sahel da kuma Yammacin Afirka.11/09/202403:41
Bakonmu a Yau
A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban daban domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya. wani lokacin kuma wasu manyan jami'an gwamnati da masu fada aji sukan kawo muna ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da suka shafe su ko kuma ci gaban kasa.