An nada sabon firaministan rikon kwarya a Pakistan
Firaministan Pakistan da jagoran 'Yan adawar kasar sun nada Anwar-rul-Haq Kakar, a matsayin fira ministan rikon kwarya, don shirya harkokin zaben da aka sanya gaba a kasar da ke fama da kalubalen siyasa da kuma tattalin arziki.
Wallafawa ranar:
Sanata kuma Dan siyasar Pakistan da ke lardin Balochistan a shiyar kudu maso yammacin kasar, zai na da ministocin sa da za su gudanar da ayyukan gwamnati har zuwa lokacin da za a zabi wanda zai dare kujerar.
A cewar ofishin Firaministan Pakistan Shehbaz Sharif ta re da jagoran ‘yan adawar kasar Raja Riaz ne suka amince da wannan nadin, don jagorantar harkokin zaben da zai gudana.
Tuni firaministan na Pakistan da jagoran ‘Yan adawar suka rattaba hannu kan wannan muhimmin shirin da za a mika ga ofishin shugaban kasar don neman sahalewar sa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu