Ko an maye gurbin Ibro a Kannywood bayan shekara 10 da rasuwarsa?
Ko an maye gurbin Ibro a Kannywood bayan shekara 10 da rasuwarsa?
A ranar Talata, 10 ga watan Disamba tauraron finafinan Hausa Rabilu Musu Ibro ke cika shekara 10 da rasuwa.
Yana kan sharafinsa lokacin da mutuwa ta riske shi a ranar Larabar 10 ga watan Disamba na 2014.
Ɗan Ibro ya yi matuƙar fice a finafinan Kannywood da aka fi sani da Camama, ko da yake ya yi finafinai a ɓangaren Santimental daga bisani.
Sai dai kamar yadda Hausawa ke cewa, "Ba rabo da gwani ba, mai da kamarsa".
A wanann bidiyon na sama, babban abiokin sana'arsa, Rabiu Daushe ya faɗa mana abubuwan da yake tunawa da mashahurin tauraron.