Ƙasashen da zaɓukansu suka ɗauki hankalin duniya a 2024

Hotunan sabin shugabanin

Asalin hoton, Many Agencies

Zaɓe wani muhimmin ginshiƙi ne ga tsarin mulkin dimokradiyya, inda ake bai wa mutane damar zaɓen shugaban da zai jagorance su.

Shekarar 2024 ta kasance shekarar da ƙasashen duniya da dama suka gudanar da manyan zaɓukansu, ciki har da waɗanda ake kallo a matsayin masu ƙarfin dimokraɗiyya.

An kuma samu ƙasashen da zaɓukansu ya ɗauki hankalin duniya a shekarar ta 2024, sakamakon irin tasirin ƙasashen a siyasar duniya ko kuma kafa wani sabon tarihi a zaɓukan ƙasashen.

A cikin wannan maƙala, mun duba wasu zaɓukan da suka ɗauki hankalin ƙasashe duniya da kuma dalilan da suka zaɓukan suka ɗauki hankali.

Nasarar Trump a zaɓen Amurka

Donald Trump

Asalin hoton, Getty Images

Ina ana batun Dimokraɗiyya, ƙasar Amurka ta yi zarra musamman yadda tsarin mulkin ya samu karɓuwa shekara aru-aru da suka shuɗe.

Ƙasar ta kasance abin koyi a fannin tsarin dimokradiyya a tsakani asashe masu tasowa da ma waɗanda ke da ci gaban.

Wannan na daga cikin dalilan da suka sanya zaɓen ƙasar ke ɗaukar hankalin duniya a duk lokacin da ake gudanar da shi.

A cikin watan Nuwamban shekara mai ƙarewar ne aka gudanar da zaɓen shugaban Amurka - wanda kuma ya ɗauki hankalin duniya kamar yadda aka saba.

An fafata a zaɓen tsakanin tsohon shugaban ƙasar Donald Trump na jam'iyyar Republican da mataimakiyar shugaban ƙasar Kamala Harris.

Bayan shafe tsawon yinin ranar 4 ga watan Nuwamba ana kaɗa ƙuri'a daga ƙarshe Donald Trump na jam'iyyar hamayya ta Republican ya samu nasara inda ya kayar da Kamala Harris ta jam'iyya mai mulki.

Faɗuwar jam'iyyar conservative a Birtaniya

Sir Kier Stammer

A ranar 4 ga watan Yulin shekarar ne aka gudanar da babban zaɓen Birtnaiya, bayan da tsohon firaministan ƙasar, Rishi Sunak ya kira zaɓen a ƙarshen watan Mayu.

Hakan na zuwa ne bayan da jam'iyyarsa ta Conservatives ta fara rasa farin jininta a ƙasar sakamakon ƙaruwar hauhawar farashin kayyaki a ƙasar.

Birtaniya na ɗaya daga cikin manyan ƙasashen duniya da tsarin dimokradiyyarsu ke da ƙarfi a faɗin duniya.

An rantsar da jagoran jam'iyyar ta Labour, Sir Keir Starmer, mai shekara 61a matsayin sabon firaministan na Birtaniya cikin watan na Yuli, inda kuma ya ci gaba da jagoranar gwamnatin ƙasar.

Nasarar mai ra'ayin kawo sauyi a zaɓen Iran

Mata

Asalin hoton, Getty Images

A ranar 28 ga watan Yuni ne al'ummar Iran suka gudanar da zaɓen shugaban ƙasa.

An yi dai zaɓen ne shekara guda kafin lokacin da ya kamata a gudanar da shi, saboda mutuwar shugaban ƙasar Ebrahim Raisi a wani hatsarin jirgi mai saukar ungulu a watan Mayu.

Kundin tsarin mulkin ƙasar ya ce dole a zaɓi sabon shugaban ƙasa kwana 50 bayan mutuwar wanda ke mulki, wanda hakan ya bai wa jam'iyyu lokaci ƙalilan na sanar da ƴan takararsu.

A zaɓen zagayen farko an kasa samun wanda ya yi nasara, inda kuma aka tafi zagaye na biyu

Ya bai wa, Saed Jalili na jam'iyar masu ra'ayin mazan jiya tazarar sama da ƙuri'a miliyan uku a zagaye na biyu na zaɓen.

Ya samu ƙuri'a miliyan 16, cikin miliyan 30 da aka kaɗa a zaɓen da mutane da dama suka ƙauracewa.

Zaɓen ya ɗauki hankalin duniya ne musamman yadda Mista Pezeshkian ya kasance mai ra'ayin kawo sauyi, saɓanin ra'ayin jagoran addinin ƙasar, Ayatollah Ali Khamenei mai ra'ayin mazan jiya.

Zarcewar Modi a zaɓen Indiya

Narendra Modi

Asalin hoton, Getty Images

A watan Yunin shekarar ne Firaministan Indiya, Narendra Modi ya kafa tarihin zama firaministan Indiya karo uku a jere.

Wani mataki da mutum ɗaya ne kawai ta taɓa kai wa a ƙasar, wato Jawaharlal Nehru, wanda ya jagoranci Indiya har tsawon shekara 16 bayan samun 'yancin kan ƙasar a 1947.

To sai dai nasarar da Mista Modi ya samu ta kasance tamkar abin nan da Hausawa ke cewa ''dakyar na tsira ya fi dakyar aka kamani''.

Jam'iyyarsa ta BJP ta rasa rinjaye a majalisar wakilan ƙasar, abin da ya sa dole ta nemi ƙulla ƙawance da wasu jam'iyyun domin kafa sabuwar gwamnati.

A tsawon lokacin mulkinsa, Mista Modi bai taɓa jagorantar gwamnatin kawance ba.

Jam'iyyar BJP ta samu kujeru 240, ƙasa da kujeru 303 da ta samu a zaɓen 2019.

Raguwar farin jinin ANC a Afirka ta Kudu

Cyril Ramaphosa

A cikin watan Mayun shekarar da muke bankwana da shi ɗin ne dai aka gudana da babban zaɓen a Afirka ta kudu wanda shi ma ɗauki hankali musamman a nahiyar Afirka.

Sakamakon zaɓen ya bai wa mutane da dama mammaki, ganin cewa jam'iyyar ANC mai mulkin ƙasar ta rasa rinjayen da take da shi a majalisar dokokin ƙasar.

Jam'iyyar - wadda Nelson Mandela ya taba jagoranta - ta samu kujeru 159 ne kacal a cikin 400.

Hakan ya yi kasa sosai idan aka kwatanta da kujeru 230 da jam'iyyar ke riƙe da su a tsohuwar majalisar dokokin ƙasar.

Sakamakon zaɓen, shi ne mafi muni ga jam'iyyar ANC tun shekaru 30 bayan kawar da mulkin wariyar launin fata - duk kuwa da cewa har yanzu jam'iyyar ita ce ta fi kowace yawan kujeru a majalisar.

Faɗuwar jam'iyya mai mulki a Ghana

A cikin watan ƙarshe na shekarar ne aka gudanar da wani zaɓen da ya ɗauki hankali musamman a nahiyar Afirka.

Zaɓen Ghana ya ɗauki hankali sosai ganin an gudanar da shi a daidai lokacin da ƙasar ke cikin halin matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa.

Ɗan takarar jam'iyya mai hamayyar, kuma tsohon shugaban ƙasar, John Dramni Mahama ne ya lashe zaɓen da gagarumin rinjaye.

Wani abu da ya ƙara burge jama'a game da zaɓen shi ne yadda ɗan takarar jam'iyya mai mulki, wanda kuma shi ne mataimakin shugaban ƙasar, Mahamudu Bawumia ya amince da shan kaye a zaɓen tun kafin hukumar zaɓen ƙasar ta kai ga sanar da sakamakon zaɓen a hukumance.

Cikin wani taron manema labarai da ya kira a gidansa, Bawumia ya ce ya kira Mahama tare da taya shi murnar nasarar zaɓen.

Wannan abu ya bai wa mutane da dama mamaki, musamman yadda yanayin siyasa Afirka take, inda 'yan takara ba su fiya amince da shan kaye ba.