Ta yaya dandalin WhatsApp ke samun kuɗi?
- Marubuci, Zoe Kleinman
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Technology editor
- Twitter,
Cikin awa 24 na rubuta sakonnin WhatsApp 100.
Babu wani mai armashi a cikinsu. Mun tsara abubuwa tare da iyalina, mun tattauna kan aiki da abokan aikina, mun gaisa da wasu, mun yi musayar labarai, mun kuma yi gulma da abokaina.
Ƙila ya kamata na sake tunani, amma yawancin sakonnin da nake da su a wayata ba su da armashi, amma kuma sakonni ne da babu wanda ya isa ya karanta su ban da mu, saboda an yi amfani da manyan na'urori masu kwakwalwa wajen ɓoye su (end-to-end encryption).
Sai kuma fa ba abu ne mai araha ba. Dandalin WhatsApp na da masu amfani da shi kusan biliyan uku a sassan duniya.
Abin tambayar shi ne ta ina WhatsApp – ko zapzap, kamar yadda matasan Brazil suke ma sa lakabi - yake samun kudi?
Maganar daya ce, ko ma yaya abin yake WhatsApp yana da uwargijiya wato kamfanin Meta, wanda ya mallaki dandalin sada zumunta na Facebook da Instagram.
Ɗaiɗikun mutane irina na samun damar yin amfani da WhatsApp a kyauta ne saboda dandalin na samun kuɗaɗe ne daga manyan kamfanoni da ke son su kai ga mutane irina.
A shekarar da ta gabata kamfanoni suka fara iya buɗe tasha (channel) a kyauta domin tura wa dubban mutane saƙonni, musamman ga wadanda suke bibiyar abubuwan da kamfanin ke yi.
Amma suna biyan wani dan kaso mai kama da na goro kafin samun damar tattaunawa da abokan huldarsu da kuma biyan kuɗi ta manhajar.
Har yanzu abin bai yi ƙarfi ba a Birtaniya. Misali a birnin Bangalore na kasar Indiya, mutum zai iya sayen tikiti hawa motar bas har ma ya zaɓi kujerar da yake so duka ta WhatsApp - kamar dai yadda ake shiga shafin intanet na kamfanonin zirga-zirgar jiragen sama ko na ƙasa.
“Burinmu shi ne samar da komai ta hanyar da ta dace, tun daga kasuwanci, mu'amala da abokan hulda ta yadda za su dinga tuntubar juna ta sassaukar hanya,'' in ji mataimakiyar shugabar fannin kasuwanci ta kamfanin Meta, Nikila Srinivasan.
“Hakan na nufin idan kana son sayen tikiti na zuwa da komawa, za ka iya biyan kuɗin zuwa da dawowa ta hanyar aikewa da sakon WhatsApp. Sai ka ci gaba da sabgoginka kawai.”
Su ma 'yan kasuwa suna da damar zaɓar tsarin sanya wurin biyan kudi a sabon madannin da aka sanya a manhajar da zai kai mutum kai-tsaye daga dandalin Facebook ko Instagram zuwa asusun kamfanin. Mis Srinivasan ta ce ana samun makudan kudade a nan.
Sai dai wasu manhajojin aika sakonni na amfani da wata hanyar ta daban.
Manhajar Signal da ta shahara da tsaro wajen tura saƙonni, masu kamfanin sun ce ba su taɓa karɓar kuɗin wani mai zuba jari ba. Tana aiki ne bisa kyautar kuɗaɗe da kamfanin ke samu daga mutane - ba kamar Telegram ba da ya dogara kan masu zuba jari.
Manhajar Discord da matasa masoya wasannin game ke amfani da ita, kyauta ake shiga amma da zarar za ka kurda wasu bangarorin ciki - kamar samun damar shiga sashen manyan wasannin game - sai ka biya wani kaso. Sannan ana yi wa masu amfani da shafin tayin mallakar katin zama mamba a dandalin wanda shi ma za ka biya wasu kudade da suka kai kusan dala 10 a kowane wata.
Kamfanin Snap, da ya samar da manhajar Snapchat na ba da damar zama mamba a a dandalin da ake kira Nitro, wanda shi ma sai an biya wasu kudade idan mutum na son yin bidiyo kai-tsaye da kuma yada shi, da 'yan alamomin nan masu kama da zanen kayan wasan yara.
A kowacce shekara Snapchat na samun kudaden shiga daga tallace-tallacen da ya ke yi da suka haura dala biliyan huɗu.
Kamfanin Element na Birtaniya na karbar maƙudan kudade daga gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu don aikewa da sakonni. Kamfanin da aka samar shekara 10 da suka gabata, na samun miliyoyi na kudaden shiga, kamar yadda mai kamfanin Matthew Hodgson ya shaidawa BBC.
Ya yi amanna yawancin manhajojin kasuwanci ba sa taka rawa kamar ake tsammani ta fuskar bunkasar kasuwanci.
“Wato fa abin da yawancin dandalin nan ke yi shi ne sayar da tallace-tallace ta hanyar bibiyar abubuwan da mutane ke so ko suke yawan ddubawa, da zarar sun shiga intanet, shikenan sai su samu wurin labewa, a yi ta tallace-tallace kamar babu gobe," in ji Hodgson.
Mr Hodgson ya kara da cewa: “Maganar duk guda daya ce, idan kai mai amfani da shafin ba ka biyan ko sisi, to hakan na nufin kai ne ka hajar dandalin.”