Dalilan da suka sa Man City ke kwasar kaya a kakar bana

Erling Haaland

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Sau ɗaya kacal Erling Haaland ya taɓa ƙwallo a da'irar yadi na 18 na Aston Villa ranar Asabar
  • Marubuci, Nick Mashiter
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport

Yanzu haka Manchester City na cikin irin yanayin da kulbo ke bi ya faɗa ƙasan gasar Premier League ta Ingila kuma babu wata alamar sassauci a nan kusa.

Kashin da ta sha ranar Asabar a hannun Aston Avilla 2-1 ya sa sun suka daga 'yan huɗun farko cikin wasa takwas da ta buga.

Saouthanmpton ce kaɗai ta fi City yawan wasannin da babu nasara cikin yawan wasannin, amma kuma idan ta samu maki ɗaya a wasanta na gaba bayan naɗa sabon koci Ivan Juric, za ta kamo City a yawan maki.

Hatta Wolves - da ta kori kocinta Gary O'Nell Lahadin da ta wuce kuma ta naɗa Vitor Pereira - ta samu ninkin makin da City ta samu a wannan tsakanin duk da cewa City ɗin ta fi ta yawan buga wasa.

Alƙaluma ne marasa daɗi ga koci Pep Guardiola ko da kuwa ya nemo hanyar rage rashin 'yanwasa irinsu Ederson, da Nathan Ake, da Ruben Dias, da kuma Rodri waɗanda duka ke jinya a yanzu.

Josko Gvardiol ya yi na bai wa Jhon Duran damar jefa musu ƙwallo a raga, ko kuma rashin ƙoƙarin Jack Grealish a wasan.

Babu mamaki a ce matsalolin rauni, ko gajiya, ko kuma kawai lokacinsu ne ya zo ƙarshe dalilan da suka jawo halin da suke ciki.

Sai dai abu ne mai wuya a yi tunanin abin da ke faruwa da su a farkon kakar nan yayin da City ke neman cin kofin Premier karo na biyar a jere.

"Babbar matsalar ita ce yawan ƙwallayen da ake zuba musu a raga," a cewar tsohon ɗan ƙwallon Ingila Alan Shearer.

"Yawan ƙwallayen da suka kwasa saboda ƙarancin tsaro a baya da kuma tsakiyar fili abu ne muhimmi. Akwai matsaloli da yawa a yanzu a kulob ɗin nan."

Sai dai Guardiola da ya bayyana a nutse yayin taron manema labarai, ya sha bamban da irin halin tasku da yake shiga idan ana buga wasa a gefen fili.

A cewarsa: "Maganin na hannunmu. Maganin matsalar ita ce mu dawo da 'yanwasan. Yanzu ɗan baya ɗaya gare mu mai lafiya, abu ne mai wuya. Za mu yi ƙoƙari a wasa na gaba - sabuwar dama kenan.

"Tabbas akwai dalilai da dama. Ana cin mu ƙwallayen da ba su kamata a ci mu ba, ba mu cin ƙwallayen da muke ci a baya. Harkar ƙwallo ba ta kaka ɗaya ba ce. Akwai kuma ƙananan dalilai."

Yanzu dai abin jira a gani shi ne irin salon da Guardiola - wanda aka sani da tsarin murza leda mafi ƙayatarwa a yanzu - zai ci gaba da bi wajen dawo da City kan ganiya.