Liverpool ta sanya Nunez a kasuwa, AC Milan na nazari kan Rashford

Darwin Nunez

Asalin hoton, Getty Images

Liverpool na shirin karɓar tayin fam miliyan 50 zuwa 60 kan ɗan wasan gabanta ɗan ƙasar Uruguay Darwin Nunez, mai shekara 25. (Football Insider)

AC Milan ita ce ƙungiya a baya-bayan nan da ke tunanin yiwuwar ɗaukar aron ɗan wasan gaban Manchester United da Ingila Marcus Rashford, mai shekara 27. (Mail)

West Ham ta tattara jerin sunayen ƴan wasan da za ta kai wa hari a watan Janairu, kuma sun haɗa da ɗan wasan gaban Brighton ɗan Jamhuriyar Ireland Evan Ferguson, mai shekara 20, da ɗan wasan Wolves da Koriya ta Kudu Hwang Hee-chan, mai shekara 28, da ɗan wasan Middlesbrough ɗa Ivory Coast Emmanuel Latte Lath, mai shekara 26. (Telegraph)

Ɗan wasan Brazil Matheus Cunha, mai shekara 25, ya kusa rattaba hannu kan sabon kwantiragi mai tsoka a Wolves duk da cewa Arsenal na kan zawarcin ɗan wasan. (Telegraph)

Randal Kolo Muani na iya barin Paris St-Germain a wannan watan, inda AC Milan da Juventus da Bayern Munich da RB Leipzig da Aston Villa da Tottenham duk suna zawarcin ɗan wasan na Faransa mai shekara 26. (Ben Jacobs)

Ɗan wasan tsakiya na Chelsea Cesare Casadei ya amince da yarjejeniyar komawa ƙungiyar Torino ta gasar Serie A, duk da cewa ƙungiyoyin ba su kammala daidaitawa kan farashin ɗan ƙasar Italiyan mai shekara 21 ba. (Gianluca di Marzio)

Galatasaray na da ƙwarin gwiwar cewa ɗan wasan Najeriya Victor Osimhen mai shekaru 26, wanda ke zaman aro daga Napoli, ba zai bar kulob ɗin na Turkiyya ba a wannan watan. (Florian Plettenberg)

AC Milan ta yi tayin ɗaukar aron ɗan wasan Barcelona Dani Olmo, mai shekara 26, na tsawon wata shida sakamakon ƙalubalen da ƙungiyar ta Sifaniya ke fuskanata wurin yi wa ɗan wasan rajista a gasar La Liga. (Corriere della Sera)

Olmo ba ya son barin Barcelona, ​​duk da cewa an tuntuɓe ta kan yiwuwar ɗaukar ɗan wasan, har yanzu ba a miƙa mata tayi a hukumance ba. (Marca)

Swansea City na cikin ƙungiyoyi da dama na Turai da ke zawarcin ɗan wasan tsakiyar Saudiiyya Abdulmalik al-Jaber, mai shekara 20, wanda ke taka leda a ƙungiyar Zeljeznicar ta ƙasar Bosnia. (TeamTalk)

Ƙungiyar Santos ta Brazil ta miƙa tayin ɗaukar ɗan wasan tsakiyar Ingila Josh Windass, mai shekara 30, daga Sheffield Wednesday. (TalkSport)